Kazalika, gazawar Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA da kuma sauran hukumomin na jihohi na sauke nauyinsu, hakan ya nuna a zahiri, na irin kalubalen da ake fuskanta, na rashin sauke nauyinsu, na bayar da agajin na gaggawa.

Misalii, an ruwaito cewa, a sansanin na ‘yan gudun hijira na Yelwata, musamman yadda suke kwana a kan tandarmin kasa, tare da kokawa da cizon Sauro, ‘ya’yansu ke ci gaba da zama a cikin yunwa, wanda hakan, ya kara harzuka su, fita yin zanga-zangar.

Bisa wasu akaluma da aka samu daga Biniwe, sun nuna cewa, a sansanin na Yelwata, an samu haihuwa 15 da kuma mata da suka samu juna biyu, su 122, wadanda kuma suke ci gaba da rashin samun kulawar kiwon lafiyarsu, hakan kuma ya jefa, rayuwar jariransu, a cikin hadari.

Bugu da kari, a sansanin ‘yan gudun hijira na jihar Nasarawa, an samu kwararowar sama da ‘yan gudun hijira guda 4,000 daga sansanin ‘yan gudun hijira na Biniwe.

Wannan ya zama wani babban nauyin wajen ciyar da su da kuma rashin samar masu da wajen wadatattun wajen kwana da rashin tsafta.

Kusan a daukacin sansanonin ‘yan gudun hijira, kamar na jihohin Borno da Adamawa, dubban ‘yan gudun hijirar da yaki da ‘yan ta’addar Boko Haram ya tarwatsa su daga matsugunan su, suna ci gaba da fuskantar karancin ruwan sha, magunguna, inda kuma ake samun barkewar Kwalara, wanda hakan, ke janyo rasa rayukan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wadannan misalan kadai, sun nuna irin rashin gazawar kula da yanayin da bil’Adama ke ciki.

Hukumar NEMA, wadda aka dora mata nauyin bayar da dauki kan aukuwar annoba, ta gaza sauke wannan nayin nata.

Sai dai, har yanzu zamu ci gaba da yin magana domin NEMA ta sauke nauyin da aka dora mata, musamman na bayar da agajin na gaggawa ga wadanda wani iftila’i, ya fada masu.

Kazalika, kayan agajin da Hukumar ta tura zuwa sansani na Yelwata, bayan kai hare-haren a yankin, idan aka yi dubi da lokacin da aka kai kayan da rashin kai wadatattunsu, wannan babban abin tambaya ne da har yanzu, ke bukatar amsa, musamman, kan yadda aka zargin wasu jami’an na NEMA, na karkatar da kayan na agajin.

Bugu da kari, hakan ya nuna irin yadda a 2024, NEMA ta fuskanci suka da zargi, na boye kayan da ya kamata a rabawa ‘yan gudun hijira a dakunanta na adana kayan agaji, wanda hakan ya jefa rayuwar ‘yan gudun hijira, musamman wadanda ke a Arewa Masu Gabas, a cikin kuncin rayuwa.

A dai jihar ta Biniwe, Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta jihar SEMA, ta fuskanci suka kan yin watsi da ‘yan gudun hijira na Yelwata, musamman duba da yadda aka barsu, a cikin kangin yunwa, cizon Sauro, wanda kuma aka yi zargin, wasu jami’an na SEMA, sun karkatar da kayan agajin, da ya kamata a raba masu.

Hakan ma batun ma yake a jihar Adamawa, inda aka zargi Hukumar SEMA ta jihar, kan kin rabar masu da kayan dauki kan lokaci, wanda hakan ya haifar da zanga-zanga a watan Mayun 2025.

Sai dai, wadanan Hukumomin suna bugewa da dora laifin kan rashin ba su kudaden da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta tura masu.

Hakazalika, rashin taka rawar da ya kamata ‘yan majalisu da matakan gwamnati ya kamata su yi, na rabar da kayan dauki ga alumma, hakan ya kara kawo rudani, kan batun na bayar da daukin.

Shirye-shiryen rabar da kayan tallafin rage radadin kuncin rayuwa, hakan ya sanya an fifita mazauna birane da ‘yan lelen ‘yan siyasa, inda su kuma ‘yan gudun hijira, aka mayar da su, saniyar ware.

A jihar ta Biniwe duk da kudaden da gwamnatin jihar kebewa da kananan hukumomin jihar da kuma wanda take kebewa sarakunan gargajiya, amma abin bakin cikin shi ne, ba kebe kudaden, da ya kamata a tallafawa ‘yan gudun hijira na jihar, inda gwamnatin ke fakewa, da cewa, tana fuskantar karancin kudade.

Karkatar da kayan agajin da ya kamata a kai wa ‘yan gudun hijirar na Yelwata, hakan ya nuna cewa, ba a dauki rayuwarsu, da wata mahimmanci ba.

Bisa ra’ayin wannan Jaridar, ya zama wajibi zababbun ‘yan majalisar kasar, su mayar da hankali wajen fifita kula da rayuwar ‘yan gudun hijira, musamman ta hanyar kebe masu wani gwa-gwaban kaso a cikin kasafin kudi na kasar da kuma kirkiro da dokokin da za su tabbatar da an yi adalci, wajen rabar masu da kayan tallafi da kuma daukar kwakwaran hukunci, ga duk wanda ya karkatar da kayan tallafin da aka yi niyyar kai masu.

Bugu da kari, ya zama wajbi matakan gwamnati uku na kasar da su kebe kudade da za a rinka taimaka wa ‘yan gudun hijira kai tsaye da ke a sansanonin su da samar masu da abinci, da kayan kula da lafiyarsu da wajen kwana da kuma sanya ido kan kayan domin a dakile yin cuwa-cuwa da kayan.

Ya zama wajbi kananan hukumomi da masarautu da gwamnatin jihohi ke tallafa masu da kudaden gudanar da ayyukansu, su yi hadaka da jagororin alummomi domin su gano tare da ganin ana tallafa wa ‘yan gudun hijirar, yadda ya dace.

Hakazalika, ya zama wajibi, a yiwa hukumomin NEMA da SEMA garanbawul, musamman domin a dawo da ainahin kimarsu, yadda ya kamata.

Zanga-zangar ta ‘yan gudun hijirar na Yelwata, wata ‘yar manuniya ce, da ke nuni da cewa, ya zama wajbi, a dauki matakan da suka wajaba, na irin halin da suke ciki.

Duba da cewa, a Nijeriya akwai ‘yan gudun hijira da yawansu ya kai sama da miliyan uku, hakan ya nuna cewa, ba wai kawai alkarin baki ya suka cancanta ba, amma kula da rayuwarsu, yadda ta kama, shi ne mafita.

Kazalika, duba da cewa, ana cikin yanayi na damina a kasar, akwai kuma wani karin barazanar da ke tafe, mai yuwa za a iya samun ambaliyar rayuwan sama wanda hakan zai janyo tarwatsa alumomi daga matsugunasu, inda hakan ya nuna cewa, tun yanzu, ya zama waji, a dauki matakan gaggawa.

Ya kamata ‘yan majalisa da shugabannin kananan hukomin da sarakunan gargajiya, su nuna cewa, da gaske suke wajen jin kan rayuwar ‘yan gudun hijira, sama da na su kudurorin na kashin kansu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yelewata yan gudun hijira na yan gudun hijirar bayar da agajin da ya kamata a hakan ya nuna wanda hakan

এছাড়াও পড়ুন:

Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila

Wakilan kasashen duniya a Majalisar Dinkin Duniya sun nuna girmamawa ga wadanda suka yi shahada a harin wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Iran

Masu fafutukar wanzar da zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka da wakilan kasashe daban-daban a Majalisar Dinkin Duniya sun gabatar da bayanai kan mutanen da suka yi shahada a hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran ta hanyar halartar hedkwatar wakilan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya.

Daruruwan masu fafutukar neman zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka ne suka hallara a hedkwatar tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin New York a ranar Litinin din wannan mako don karrama shahidan harin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta kai kan kasar Iran, inda suka rattaba hannu kan littafin tunawa da nuna juyayi ga gwamnatin Iran da al’ummar kasarta.

Mambobin kungiyar Yahudawa ta kasa da kasa Neturei Karta, kungiyar Yahudawa masu adawa da ‘yan sahayoniyya, su ma sun halarci gangamin tare da nuna girmamawa ga wadanda harin ya rutsa da su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • SON Ta Bada Shaidar Ingancin Kayayyaki Ga Wasu Kamfanoni A Kaduna
  •   Gaza: Fiye Da Falasdinawa 17 Ne Su Ka Yi Shahada Ayau Juma’a
  • Janar Ali Fadli: IRGC Suna Da Damar Kera Makamin Nukiliya Da Kuma Rufe Mashigar Ruwan Hurmuz
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Sake Aiwatar Da Kisan Kare Dangi Kan ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
  • Kasar Iran Ta Nuna Ire-Iren Makamai Masu Linzami Da Ta Mayar Da Martani Da Su Kan ‘Yan Mamaya
  • Karamar Hukumar Maru Ta Bukaci A Dauki Matakan Kariya Kan Cutar Kwalaraci
  • Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila
  • Uwargidar Gwamnan Kaduna Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Noma Ga Mata Manoma