’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC
Published: 3rd, July 2025 GMT
A ci gaba da sauya sheƙar da ’yan Majalisar Wakilai na Tarayya ke yi a ranar Alhamis wasu mambobi bakwai daga Jihar Akwa Ibom sun sanar da sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.
Cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da shida daga Jam’iyyar PDP da kuma ɗaya daga Jam’iyyar YPP.
’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar Tinubu – Amaechi Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaroShugaban Majalisar Wakilan Tarayya Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙunsu na sauya sheƙa a zauren Majalisar a ranar Alhamis yayin zaman majalisar.
’Yan majalisar dai sun yi nuni da ƙara samun rarrabuwar kawuna da rigingimun cikin gida a cikin Jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya sa suka yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar.
Waɗanda suka sauya sheƙa daga PDP sun haɗa da: Paul Ekpo da Unyime Idem da Martins Etim da Okpolu Ukpong Etteh da Uduak Odudoh da Okon Ime Bassey.
Shi ma ɗan Majalisa Emmanuel Ukpong-Udo na Jam’iyyar YPP ya koma APC.
’Yan majalisar dai sun ce rikicin da ya ɓarke a Jam’iyyar PDP a Akwa Ibom da ma ƙasa baki ɗaya ya sa ba su iya wakiltar mazaɓarsu yadda ya kamata.
Ficewar ta zo ne makonni kaɗan bayan gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya koma APC.
Da yake mayar da martani game da sauya sheƙar, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda ya nuna baƙin cikinsa game da ci gaban da aka samu.
Chinda ya ce, iƙirarin rarrabuwar kawuna a cikin Jam’iyyar PDP bai dace ba kuma ya saɓawa doka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Akwa Ibom Jam iyyar PDP Yan majalisar Yan Majalisar sauya sheƙa a Jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo.
Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida.
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDPMai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada.
Sai dai a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar da yammacin ranar Juma’a, kakakinta na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar ba za ta dakatar da shirin gudanar da taron ba.
Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin tauye haƙƙin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ologunagba, ya ce hukuncin ba zai hana PDP ci gaba da shirye-shiryenta na zaɓen sabbin shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa ba.
Ya yi nuni da cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa jam’iyyu na da ’yancin tafiyar da harkokinsu na cikin gida.
“PDP na kira ga mambobinta da shugabanni a faɗin ƙasar nan da su kuma ci gaba da shirye-shiryen babban taron jam’iyyar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar mai bin doka ce, kuma ta umarci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara game da hukuncin kotun.