Janar Ali Fadi wanda tashar talabijin din Iran ta yi hira da shi a jiya da dare, ya bayyana cewa; Iran tana da damar kera makamin Nukiliya da kuma rufe mashigar ruwan Hurzum.

Janar Fadli ya ce; Dakarun na kare juyin musulunci sun lakanci yadda ake kera shi, tare da bayyana fatan cewa kar  makiya su tafka  babban kuskuren da zai tura Iran yin tunanin hakan.

Dangane da batun rufe mashigar ruwan Humuz kuwa, janar Faldi ya ce, suna da damar yin hakan,sai dai kuma ko kadan wannan ba ya cikin manufofin jamhuriyar musulunci.

Janar Fadli shi ne mai kula da tafiyar da ayyyuka a tsakanin bangarori daban-daban na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila Zata Gamu Da Maida Martani Mai Tsanani Idan Ta Kuskura Ta Sabonta Yaki Da Iran

Babban hafasan hafsoshin kasar Iran Major General Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta sabonta yaki da kasar Iran ta zata fuskanci maida martani mafi tsanani.

Janar Musawi ya bayyana haka ne a jiya laraba a lokacinda yake hira da tashar talabijan ta almayaden ta kasar Lebanon

Ya kuma kara da cewa a yakin da ya gabata wato wa’adussadik na ukku na watan da ya gabata, sojojin Iran basu fitar da dukkan makamansu su. Ko kuma dukkan karfinsu ba. Don haka idan yahudawan sun  kukura sun sake farfado da yaki da JMI sai sun hadu da martani wanda ya fi na farko zafi,

Janar Musavi ya kara da cewa HKI ta dauki shekaru tana tanajin ranar da yaki zai hadata da JMI, kuma ta ga inda tanadinta yak are. Ya ce abinda yake gaba gareta ya fi muni idan bata sani ba ta sani.

A wabi bangare Janar Musawi ya bayyana cewa kasashen yamma da kuma HKI sun son amfani da shirin makamashin nukliya na kasar Iran don raba kasar Iran da kuma maida ita fiye da yadda take a zamanin nsarki sha. Amma tare da taimakon All..sun kasa yin haka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jalali: Mun  Hana Fitowar Sanadarorin Nukiliya Ta Hanyar Aiki Da Ka’idojin Tsaro
  • Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
  • Isra’ila Zata Gamu Da Maida Martani Mai Tsanani Idan Ta Kuskura Ta Sabonta Yaki Da Iran
  •  Muhsin Rizai: Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Bayar Da Umarni  Da Jagorantar Yakin “Wa’adussadiq 3”
  •  Arakci Ya Mayar Wa Da Jami’ar Harkokin Wajen ” EU” Martani
  • Mujallar “Foreign Policy”Ta Amurka: Isra’ila Ba Ta Yi Nasara A Yaki Da Iran Ba
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Irin Aniyar Da Gwamantinsa Ta Kudurta Wajen Kare Tsaron Kasa Da Al’ummarta
  • Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
  • Rasha Ta Jaddada Aniyarta Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran