Kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke naɗin Sanusi II ba — Gwamnatin Kano
Published: 15th, March 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba.
Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotun kawai ta dakatar da aiwatar da hukuncinta har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar.
Ya jaddada cewa kawai Kotun Ƙoli ce ke da ikon sauya hukuncin mayar da Sanusi kan karagar mulki.
“Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke hukuncinta na baya ba. Kawai dai ta dakatar da aiwatar da shi har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe,” in ji Dederi yayin da yake magana da manema labarai.
Ya ƙara da cewa kotun ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar na da hurumin dawo da Sanusi kan sarautar Kano.
“Hukuncin da aka yanke a ranar 10 ga watan Janairu ya tabbatar da cewa Kotun Tarayya ta farko ba ta da ikon yanke hukunci kan wannan batu.
“Sanusi na nan a matsayin Sarki har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci,” in ji shi.
Shari’ar ta samo asali ne bayan Aminu Baba DanAgundi, ɗaya daga cikin magoya bayan tsohon Sarki Aminu Ado Bayero, ya garzaya kotu tare da ƙalubalantar dawo da Sanusi a matsayin Sarkin Jihar.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukunci cewa komai zai ci gaba da kasancewa yadda yake har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe kan lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatinl Rikicin Masarauta har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta.
A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025.
Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai.
Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin biyan fansho.
Ya kara da cewa, wannan yunkuri ya yi daidai da kudirin jihar gwamnati na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki, tare da bai wa ‘yan fansho dama su gyara duk wani bayanin da bai cika ba a takardunsu.
Shi ma da ya ke jawabi, Akanta Janar na Jihar, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ya jaddada cewa aikin tantancewar zai bai wa ‘yan fansho damar sabunta bayanansu da suka bace ko suka canza a takardunsu.
Saboda haka, ya bukaci dukkan ‘yan fansho daga ma’aikatun gwamnati, sassan hukumomi, kananan hukumomi da kuma hukumomin ilimi na kananan hukumomi da su halarci tantancewar a ranar da aka tsara kamar yadda yake cikin jadawalin aikin.
A jawabinsa, Shugaban kungiyar kananan hukumomi ALGON ta Jihar Jigawa, Farfesa Salim Abdurrahman, ya tabbatar da cikakken goyon baya daga shugabannin kananan hukumomi 27 domin cimma burin aikin.
Shugaban na ALGON wanda shugaban karamar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani ya wakilta, ya bukaci ‘yan fanshon da su ba da cikakken haɗin kai don samun nasarar shirin.
Shi ma Shugaban hukumar, Dr. Bilyaminu Shitu Aminu, ya bukaci ‘yan fansho daga sassa daban-daban da su ba da hadin kai domin cimma burin da aka sanya, tare da jaddada cewa su ziyarci sakatariyar kananan hukumominsu domin a tantance su.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, Alhaji Umar Sani Babura, ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta bada cikakken goyon baya domin nasarar wannan shiri.
Dukkan ‘yan fansho daga Ma’aikatun Gwamnati, Kananan Hukumomi, da Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi da ke cikin tsarin fanshon, ya zama wajibi su halarci wannan tantancewa a ranakun da aka tsara a jadawalin aikin.
Usman Muhammad Zaria