A Yau Juma’a Ne Ake Gudanar Da Taron Karrama Shahid Birgediya Janar Husain Salami A Nan Birnin Tehran
Published: 4th, July 2025 GMT
Taron nay au dai an ba shi taken; Girmama Kwamandan Farmakin ” Wa’adussadiq” za kuma a yi shi ne da marecen yau a birnin Tehran a Husainiyyar ” Fatimatuzzahra ( a.s) dake karkashin rundunar soja ta ” Arrasulul-Muhammad ( a.s).
Shi dai Birgediya Shahid Hussain Salami ya yi shahada ne a wani harin ta’addanci da HKI ta kawo wa Iran a ranar 13 ga watan Yuni tare da wasu kwamandoji da soja.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin
A yau Talata ne gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya gudanar da bikin daga tuta, da bikin murnar cika shekaru 28 da dawowar yankin musamman na HK karkashin ikon kasar Sin.
Da yake jawabi yayin taron, kantoman yankin Lee Ka Chiu John, ya ce tun bayan kama aikinsa, gwamnati mai ci a HK, ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye don gina yanki mai tsaro da daidaito, tare da zage damtse wajen gina tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’ummarsa, kuma sannu a hankali matakan na haifar da mai ido.
Lee ya ce, a nan gaba, zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da samun ci gaba mai inganci, da managarcin yanayin tsaro, kana zai gaggauta bunkasa yankin arewacin yankin, da kara azamar kyautata rayuwar jama’ar HK. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp