A wani ɓangaren kuma, rundunar Operation DELTA SAFE ta bankaɗo da kuma karɓo danyen mai da aka sace wanda ya kai darajar Naira biliyan 3.5. Haka kuma, an karɓo lita 2,381,239 na ɗanyen mai, lita 605,393 na man diesel da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, lita 41,465 na man fetur DPK da kuma lita 26,905 na Fetur.

Rundunar ta lalata haramtattun wuraren tace man 174, tare da kwace motoci 45 da makamai da nakiya iri-iri da aka shirya domin tayar da su.

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Army

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 30 da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa.

Kakakin ’yan sandan Jigawa, SP Lawan Shi’isu, ya ce matashin mai suna Hussaini Abubakar ana zargin ya kashe mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75 da misalin karfe 8 na yammacin ranar 29 ga watan Yunin 2025.

Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina

SP Shiisu ya ce matashin ya jikkata mahaifiyarsa da bulon ƙasa, kuma bayan an garzaya da ita asibiti ta mutu washegari.

Ya ce wannan lamari ya sanya rundunar ta gaggauta tura tawagar jami’ai kuma aka cafke matashi da a yanzu haka an soma gudanar da bincike a kan lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP AT Abdullahi, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin rashin imani na kololuwa.

Ya bai wa al’umma tabbacin cewa za su bi diddigin lamarin domin matashin ya girbi hukunci daidai da abin da ya aikata.

Rundunar ’yan sandan ta bukaci jama’a da su rika gaggauta mika rahoton duk wata alama ta tabin hankali ko cin zarafi domin kaucewa faruwar makamancin wannan lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA
  • Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami
  • ’Yansanda Sun Ceto Ɗan Ghana, Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3
  • Yawan Kudin Shiga Da Sin Ta Samu A Fannin Sana’ar Manhaja A Watanni 5 Na Farko Na Bana Ya Wuce Yuan Triliyan 5.5
  • Aragchi: Iran Ba zata Taba Daina Tace Makamashin Uranium A Cikin Gida Ba
  • ’Yan sanda sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa
  • Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 a Borno
  • Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara
  • Manomi Ya Ceto Jaririya Da Aka Binne Da Ranta A Kebbi