Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [7]
Published: 15th, March 2025 GMT
1. Godiya da harshe:
Wannan yana nufin yabon Allah da faɗar ni’imominsa da kuma ambatonsa a cikin kalmomi. Wannan yana da muhimmanci saboda yana nuni da cewa mutum ya gane cewa Allah ne mai bayar da ni’ima. Hadisin da aka kawo yana nuna cewa mutum idan ya bayyana ni’imomin Allah, to yana cikin masu godiya.
2. Godiya da gaɓɓai:
Wannan yana nufin amfani da dukkan gabban jiki wajen yin biyayya ga Allah da nisantar saɓon Sa. Misali, idan mutum yana da lafiyar jiki, to ya yi amfani da lafiyar wajen aikata kyawawan ayyuka kamar sallah, azumi, sadaƙa, da taimakon jama’a. Idan kuma mutum yana da arziki, ya yi amfani da shi wajen tallafa wa marasa hali da hidimtawa addini. Wannan yana tabbatar da cewa godiya ga Allah ba kawai yana cikin harshe ba, har ma yana cikin aiki.
3. Godiya da zuciya:
Wannan yana da alaƙa da imani da ilimi. Yana nufin mutum ya gane cewa duk wata ni’ima daga Allah take, ba wai saboda ya cancanta a ba shi ba saboda wani abu da ya yi wa Allah, a a sai dai domin Allah yana da rahama da falala da jin ƙai. Wannan yana hana girman kai da alfahari, domin mutum zai fahimci cewa Allah Yana bayar da ni’ima a matsayin kyauta, ba lallai ne saboda ibadarsa ba. Wannan yana ƙarfafa tawali’u da jin haƙuri idan mutum bai samu abin da yake so ba.
A taƙaice, maganar Ibnu Juzai tana koyar da cewa godiya ba kawai fadar “Alhamdulillahi” ba ce kawai, a a, tana da sassa guda uku: da suka haɗa da harshe, da aiki, da kuma zuciya. Idan mutum yana godiya ta waɗannan hanyoyi, to zai zama cikakken mai godiya ga Allah. Wannan yana ƙarfafa imani, yana ƙara ni’ima, kuma yana kusantar da bawa ga Ubangijinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan Wannan yana
এছাড়াও পড়ুন:
An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno
Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke kiwon shanu, ya samu rashin jituwa da Jauro Ishaya mai shekaru 43, kan rikicin filin kiwo.
A cewar majiyar, yayin takaddamar ne aka zargi Jauro Ishaya da harba bindigar gida wadda ta sami Alhaji Usman a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Askira, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta kama wanda ake zargi, kuma tana ci gaba da kokarin kwato bindigar da aka yi amfani da ita a lamarin.
Majiyoyi sun kara da cewa, sashen binciken manyan laifuka (CID) na rundunar ’yan sanda a Maiduguri ya fara gudanar da bincike kan lamarin.