Dele Momodu, sanannen ɗan jarida kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa yawancin magoya bayan jam’iyyar sun fara ficewa daga cikinta, suna barin tsarin jam’iyyar a hannun ministan babban birnin tarayya. Dele ya bayyana hakan ne yayin wani shiri a Channels TV, inda ya nuna cikakken goyon bayansa ga sabon ƙawancen jam’iyyun adawa da suka rungumi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin fuskantar zaɓen 2027.

Momodu ya ce, duk da Wike yana PDP, kasancewarsa a gwamnatin APC na nuna rashin amanna kuma ya janyo rikici cikin jam’iyyar. A cewarsa, “mutane suna barin gawar PDP ga Wike da ƙawayensa kawai.” Ya zargi APC da shirya makirci na tura mutanenta cikin jam’iyyun adawa don rage musu ƙarfi a 2027, yana mai cewa APC na ƙoƙarin hana gasa mai tsabta a gaba.

Tinubu Ya Sasanta Wike, Fubara, Da Ƴan Majalisar Ribas Duk Da Cewa Wike Ba Ɗan APC Ba Ne Amma Muna Jin Daɗin Aikin sa – Tinubu

Ya bayyana cewa sabon ƙawancen da aka kafa a ƙarƙashin ADC ya ba shi sabon fata game da makomar Nijeriya, yana mai cewa ko a lokacin ƙawancen da ya tallafa wa Buhari a 2014 da 2015, ba a samu irin wannan haɗin kai da tasiri ba. Ya ce wannan mataki ne na ceto Nijeriya daga hannun mutum guda da ke ƙoƙarin mallake ƙasar gaba ɗaya.

Momodu ya kuma sukar gwamnatin Tinubu, yana mai cewa Nijeriya ta ƙara taɓarɓarewa fiye da lokacin mulkin Buhari. Ya tambayi ‘yan Nijeriya ko halin da ake ciki a yau ya fi na shekaru biyu da suka wuce, yana mai cewa gwamnatin yanzu ta gaza wajen sauke nauyin da ke kanta. Ya bayyana ficewarsa daga PDP a matsayin wani mataki na neman sabuwar mafita ga ƙasar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yana mai cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu Ta Yanke Wa Ɗan TikTok Tsulange Hukuncin Ɗauri Kan Shigar Zubar Da Mutunci

Wata Kotun Majistare da ke jihar Kano ta yanke wa fitaccen ɗan TikTok, Umar Hashim da aka fi sani da Tsulange, hukuncin ɗauri na shekara ɗaya bisa laifin aikata abinda ya saɓa da tarbiyya a bainar jama’a.

Alƙaliyar kotun, Hadiza Muhammad Hassan, wadda ke zaune a Gyadi Gyadi, ta samu Tsulange da laifi na zubar da mutunci a idon jama’a bayan gabatar da hujjoji da shaidu. Ta bayyana cewa an tabbatar da cewa ɗan TikTok ɗin ya aikata laifin ne cikin gangan.

Ɗan TikTok Tsulange Ya Shiga Hannu Bisa Wanka Da Rigar Mama A Titi Kotu Ta Tura Ɗan Tiktok Gidan Yari Kan Shigar Mata Da Kalaman Batsa A Kano

A hukuncin da ta yanke, ta ba da umarnin da a ɗaure shi na tsawon shekara guda, ko kuma ya biya tarar Naira 80,000 a matsayin madadin ɗaurin. Haka kuma, kotun ta umarce shi da ya biya hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Naira 20,000 don rage kuɗin bincike da shari’ar da aka yi.

Rahoton LEADERSHIP ya nuna cewa an gurfanar da Tsulange ne a watan Yuni 2025 bayan hukumar ta kama shi kan wani faifan barkwanci da ya ɗauka yana wanka a titi yana sanye da kayan mata a matsayin wani ɓangare na wasan kwaikwayo.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bayan Taron Haɗaka, Hankali Wike Ya Tashi — ADC
  • Kotu Ta Yanke Wa Ɗan TikTok Tsulange Hukuncin Ɗauri Kan Shigar Zubar Da Mutunci
  • Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad
  • Abubakar Malami Ya Fice Daga APC, Ya Koma ADC
  • David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu
  • Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang
  • Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Cewa: Ba Za A Iya Kawar Da Fasahar Nukiliya Da Karfi Ba
  • Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara