Antonio Guterres Ya Kadu Saboda Mummunan Halin Da Falasdinawan Gaza Suke Ciki
Published: 4th, July 2025 GMT
Babban magatakardar MDD Antonio Gutress ta sanar da kaduwarsa da kuma jin haushin yadda wahalhalun Falasdinawa a Gaza suke karuwa, yana mai cewa: Sauran abinda ya rage da zai rike rayuwa a Gaza, ya kusa karewa saboda rufe hanyoyin da suke shiga Gaza da HKI ta yi.
Kakakin babban magatakardar na MDD Stephen Dujarric, ne ya ambato maigidan nasa yana fadin haka akan yanayin da zirin Gaza yake ciki, tare da kuma da cewa; MDD tana son ganin an bai wa fararen hula kariya da kuma biya musu bukatunsu.
Antonio Guterres ya kuma bayyana firgitarsa a lokaci daya kuma da bacin ransa akan yadda Falasdinawan Gaza su ka cikin mawuyacin hali, yana mai kara da cewa da akwai adadi mai yaw ana Falasdinawan da aka kashe a cikin kwanakin bayan nan saboda hare-haren Isra’ila a cikin sansanon da ‘yan hijira suke rayuwa a ciki, haka nan kuma Falasdinawan da suke kokarin samun taimakon abinci.
Babban magatakardar MDD ya yi Allawadai da kashe fararen hula yana mai kara da cewa; A cikin wannan makon kadai, Falasdinawan da su ka yi hijirar dole sun kai 30,000 bayan da Isra’ila ta umarce su, su fice daga yankunansu a ranar Lahadin da ta gabata.
Hakan nan kuma Guttress ya ambaci rashin mafaka da abinci a Gaza, kuma babu magunguna da ruwan sha.
Bugu da kari ya ce yanzu an dauki makwanni 17 ba a shigar da makamashi cikin yankin na Gaza ba, tare da cewa, abinda yake rike rayuwa a cikin yankin yana gab da karewa.
Tun a watan Oktoba na 2023 ne dai HKI take tafka laifukan yaki akan al’ummar Falasdinu babu kakkautawa. Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 100,000, wadanda su ka jikkata dubun dubata ne, mafi yawancinsu mata da kananan yara.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Falasdinawan da
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq.
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoSun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi.
A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Saudiyya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya bayar da cikakken goyon baya wajen ganin an saki waɗanda aka kama.
Bincike ya gano cewa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi ne a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, suka ƙwayoyin a jakunkuna waɗanda aka kama.
Mutanen uku da aka kama, sun tashi a jirgin Ethiopian Airlines a ranar 6 ga watan Agusta don yin Umara, amma aka kama su a Saudiyya.
Binciken NDLEA ya kai ga kama wani shugaban masu safarar miyagun ƙwayoyin, mai shekaru 55, Mohammed Ali Abubakar (wanda aka fi sani da Bello Karama).
Hakazalika, hukumar ta kama wasu mutum uku ciki har da ma’aikatan jirgi.
Mutanen da aka kama su ne suka shirya safarar ƙwayoyin a jakunkunan mutane da aka kama a Saudiyya.
NDLEA ta gabatar da shaidun da suka tabbatar da cewa mutanen da aka kama a Saudiyya ba su da laifi.
Sakamakon haka, hukumomin Saudiyya suka sako ɗaya daga cikinsu a ranar 14 ga watan Satumba, sannan suka sako sauran biyun a ranar 15 ga watan Satumba.
Babafemi, ya ce Marwa ya gode wa hukumomin Saudiyya saboda mutunta yarjejeniyar haɗin kai tsakaninsu da Najeriya.
Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu da sauran manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Shari’a, Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Ministan Sufurin Jiragen Sama, da Mai Bai Wa Shugaba Shawara Kan Harkar Tsaro, saboda gudummuwarsu.
Ya ƙara da cewa wannan lamari ya nuna cewa Najeriya tana tsayawa wajen kare ‘yan ƙasarta a ƙasashen waje kuma ba za ta yadda wani ɗan Najeriya ya sha wahala saboda laifin da bai aikata ba.