Fitar Da Nama Zuwa Saudiyya: Mayankar Dabbobi Ta Jurassic Ta Yi Hadin-gwiwa Da Shirin CDI
Published: 15th, March 2025 GMT
Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare.
“Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara habaka fitar da ingantaccen nama zuwa ketare”, in ji Oroh.
Kazalika, an bijiro da wannan hadaka ce, sakamakon yadda Saudiyya ta nuna sha’awarta, na son shigar da nama zuwa kasarta daga Nijeriya, wanda ya kai tan 176,000 a duk shekara, tare da kuma ciyawar dabbobi ta alfalfa hay da abincin dabbobi da ake sarrafawa da kuma Waken Soya.
A yanzu haka, CDI na ci gaba da tattaunawa da SALIC, musamman domin cimma bukatar samar da naman, wanda hakan zai kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.
Wannan hadaka a tsakanin sauran sassan gwamnati daban-daban da CDI ke jagoranta, manufar ita ce; domin fitar da nama ketare kimanin tan 35,200 zuwa karshen 2025.
Bugu da kari, masu ruwa da tsaki a sassan kula da ayyukan kula da dabbobi da kwararrun likitocin dabbobi, duk an sanya su a cikin wannan aiki.
Aikin mayankar na Jurassic, ya kai na dala miliyan 10; wanda kuma ake gudanar da shi a hekta 50 da ke Nasarawa Egon, cikin Jihar Nasarawa.
Ana sa ran, za a kammala wannan aikin a watan Satumban 2025, inda wajen aikin zai dauki yawan Shanun da za a yanka da suka kimanin 1,000 da kuma Akuyoyin da za a yanka a kullum.
Kazalika, aikin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi na kai tsaye, sama da 20,000 da kuma ayyukan yi wadanda ba na kai tsaye ba, kimanin 100,000 tare da kara bunka tattalin arzikin Nijeriya da kuma daga darajar Naira.
A shirin fitar da Naman, an kiyasta samar da kudin shiga da ya kai kimanin dala miliyan 273, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 451 kafin zuwa 2025.
Wannan hadakar ta nuna irin kokarin da Nijeriya ke yi, duba da cewa; hakan zai kara wajen ganin ana amfana da fannin na aikin noman, tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasaAn ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.
Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.
Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.
“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.
Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.