HausaTv:
2025-07-04@12:31:02 GMT

  Gaza: Fiye Da Falasdinawa 17 Ne Su Ka Yi Shahada Ayau Juma’a

Published: 4th, July 2025 GMT

Daga safiyar yau juma’a, Falasdinawa 17 sun yi shahada sanadiyyar hare-haren da HKI ta kai wa Falasdinawa ‘yan hijira a yankin Mawasi dake Kudancin Khan-Yunus.

Tun da safiyar yau ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a gabashin birnin Gaza, haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun yi amfani da jirgin sama maras matuki nau’in Code Copter ” wajen bude wuta akan wannan yankin.

A cikin unguwar Shuja’iyya kuwa, sojojin sahayoniyar sun tarwatsa da rusa gidajen Falasdinawa.

A sansanin ‘yan hijira na Jabaliya dake arewacin Gaza ma dai jiragen yakin HKI sun kai jerin hare-hare masu tsanani da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu.

A daren jiya Alhamis ‘yan sahayoniyar sun yi kisan kiyashi akan Falasdinawan da suke cikin sahun jiran samun taimakon abinci da hakan ya yi sanadiyyar shahadar adadi mai yawa daga cikinsu.

Asibitin ” al-Shafa” ya sanar da cewa, an sami shahidai 11 da su ka hada kananan yara da mata a wani sabon kisan kiyashi da ‘yan sahayoniyar su ka yi wa makarantar ‘almustafa’ dake kunshe da ‘yan hijira a yammacin birnin Gaza.

A kusa da masallacin al-Aqqad’ a yankin Mawasi dake Khan-Yunus Falasdinawa 13 ne su ka yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa ya jikkata sanadiyyar harin jirgin sama na yaki. Kwanaki 3 kenan ajere da adadin Falasdinawan da suke yin shahada a akowace rana yana haura 100, mafi yawancinsu kananan yara ne da mata.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: sahayoniyar su

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa Yahudawan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai ban tsoro ya bayyana cewa: Manyan kamfanoni suna da hannu wajen aiwatar da kisan kare dangi a Gaza

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana sunayen wasu manyan kamfanoni na duniya sama da 60 da ke da hannu a tallafawa wajen gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida a yankunan gabar yammacin kogin Jordan da kuma hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza.

Rahoton wanda wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, ta wallafa ya samo asali ne daga bayanai sama da 200 daga kasashe, kungiyoyin kare hakkin bil adama, masana ilimi da kamfanoni. Ta yi kira ga kamfanonin da su daina kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila, ta kuma yi tambayar cewa saboda rike harkokin gudanarwar kudade da kuma doka da oda don fa’idarsu da suke samu daga hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa yankunan Falasdinawa.

Daga cikin kamfanonin da aka ambata a cikin rahoton, mafiya shahararsu akwai kamfanonin Amurka: Google, Microsoft, IBM, Caterpillar, a heavy equipment manufacturer, Lockheed Martin, a military manufacturer, da Hyundai na kasar Koriya ta Kudu. Rahoton ya zarge su da hannu a ayyukan danniya, kera makamai, da lalata dukiyoyi a yankunan Falasdinu.

Rahoton yana wakiltar fadada jerin sunayen da aka baiwa  Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 2023 wanda ya mayar da hankali kawai kan kamfanonin da ke da alaka gwamnatin mamaya, yayin da sabon rahoton ya kunshi bangarori masu fadi da ke da alaka da cin zarafi a Gaza. Albanese ta gabatar da wannan zargi a cikin wani cikakken bayani game da rikicin Falasdinu: “Yayin da ake kashe rayuka a Gaza kuma ake ci gaba da kara kashe-kashen a gabar yammacin kogin Jordan, wannan rahoto ya nuna cewa kisan kiyashin da ake kira ya ci gaba ne kawai saboda yana da riba ga bangarori da yawa.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace
  •  A Yau Juma’a Ne Ake Gudanar Da Taron Karrama Shahid Birgediya Janar Husain Salami A Nan Birnin Tehran
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa ‘Yan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa Yahudawan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Sake Aiwatar Da Kisan Kare Dangi Kan ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa
  • Falasdinawa Kimani 40,000 HKI Ta Kora Daga Yankin Yamma Da Kogin Jordan
  • Ben Gafir Ya Bukaci Gwamnatin HKI Ta Mamaye Yankin Gaza Gaba daya
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Luguden Bama-Bamai Kan Falasdinawa Da Suka Janyo Shahada Da Jikkata
  • Aragchi: Hare-Haren HKI Ya Kara Rashin Zaman Lafoya A Yankin Yammacin Asiya