Kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin Iran sun shirya tsaf don kare juyin juya halin Musulunci da kasarsu

A yayin ziyarar da ya kai wa iyalan shahidi kwamandan tsaron cikin gida na kasar Iran Kanal Mohammad Alizadeh; Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Jajirtattun sojojin kasar Iran a shirye suke da dukkanin karfinsu wajen kare kyawawan manufofin juyin juya halin Musulunci da kuma dukkanin yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin kowane irin yanayi da kuma fuskantar duk wani mai neman wuce gona da iri.

Manjo Janar Amir Hatami, babban kwamandan sojojin kasar Iran, tare da rakiyar Hujjatul-Islam Ahmad Jalili Safat, mataimakin shugaban bangaren rukunan siyasa ta sojojin kasar, Manjo Janar Muhammad Yousufi Khosh-Qalb, mataimakin kodinetan sojojin sama, da Hujjatul-Islam Muhammad Bahman, shugaban sashen siyasa na bangaren sojan sama, Muhammad Ali sun ziyarci gidan shahidi jajirceccen mayakin rundunar sojin saman Iran kanal Muhammad Ali Zadeh, inda suka gana da iyalan wannan shahidi mai girma tare da girmama matsayin daukakarsa na samu shahada.

A yayin wannan ziyarar, Manjo Janar Hatami ya mika sakon taya murnar shahadar narigayi da ta’aziyyar tashinsa, gami da tunawa da wannan shahidi daga rundunar sojojin sama da dukkan sauran shahidai masoya masu girma da suka sadaukar da kansu a lokacin wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kawo hare-haren ta’addanci kan Iran. Yana mai jaddada cewa: Shahadan bayin Allah salihai a cikin wannan harin wuce gona da iri, ya nuna girman ta’addancin makiya masu dauke da ruhin zalunci, kuma lallai sun tarar da jajirtattun gwarazan Iraniyawa da suka sadaukar da kansu domin kare al’umma da kasarsu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: sojojin kasar Iran Manjo Janar

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila Zata Gamu Da Maida Martani Mai Tsanani Idan Ta Kuskura Ta Sabonta Yaki Da Iran

Babban hafasan hafsoshin kasar Iran Major General Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta sabonta yaki da kasar Iran ta zata fuskanci maida martani mafi tsanani.

Janar Musawi ya bayyana haka ne a jiya laraba a lokacinda yake hira da tashar talabijan ta almayaden ta kasar Lebanon

Ya kuma kara da cewa a yakin da ya gabata wato wa’adussadik na ukku na watan da ya gabata, sojojin Iran basu fitar da dukkan makamansu su. Ko kuma dukkan karfinsu ba. Don haka idan yahudawan sun  kukura sun sake farfado da yaki da JMI sai sun hadu da martani wanda ya fi na farko zafi,

Janar Musavi ya kara da cewa HKI ta dauki shekaru tana tanajin ranar da yaki zai hadata da JMI, kuma ta ga inda tanadinta yak are. Ya ce abinda yake gaba gareta ya fi muni idan bata sani ba ta sani.

A wabi bangare Janar Musawi ya bayyana cewa kasashen yamma da kuma HKI sun son amfani da shirin makamashin nukliya na kasar Iran don raba kasar Iran da kuma maida ita fiye da yadda take a zamanin nsarki sha. Amma tare da taimakon All..sun kasa yin haka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zamfara Babban Wuri Ne Na Aikin Noma Mai Amfani Da Hasken Rana – Gwamna Lawal
  • Isra’ila Zata Gamu Da Maida Martani Mai Tsanani Idan Ta Kuskura Ta Sabonta Yaki Da Iran
  • An Gudanar Da Taron Girmama Shahidan Yakin Kwanaki 12 A Nan Tehran
  •  Muhsin Rizai: Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Bayar Da Umarni  Da Jagorantar Yakin “Wa’adussadiq 3”
  • Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Luguden Bama-Bamai Kan Falasdinawa Da Suka Janyo Shahada Da Jikkata
  • Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila
  • Wargajewar HKI Ba Makawa Inji Wani Janar Daga Sojojin JMI
  • Laftanar Kanar Shikarci: Sojojin Iran Suna Cikin Shirin Ko-Ta-Kwana Fiye Da Kowane Lokaci