Iran Ta Yi Tir Da HKI Da Kokarin Wanke Kanta Tare Da Rabawa Addinin Musulunci Ta’addanci
Published: 15th, March 2025 GMT
Jakadan JMI na din din din a MDD Amir Saeed Iravani ya yi tir da HKI kan yadda take amfani da Kalmar “ta’addancin Addinin musulunci’ don rabawa addinin ayyukan ta’addanci.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Iravani yana fadar haka, a taron yaki da kin addinin musulunci a kasashen yamma da kuma kasashen da suke fama da karancin sanin addinin musulunci a duniya.
Iravani ya kara da cewa, shekaru uku da suka gabata ne babban zauren MDD ya samar da kuduri mai lamba 73/254 don yaki da kin musulmi da addinin musulunci a duniya. Jakadan ya yi tir da Banyamin Natanyahu Firai ministan HKI da yawan amfani da kalmomi wadanda suke rabawa addinin musulunci ayyukan ta’addanci.
A jiya Jumma\a 14 ga watan Maris na ko wace shekara ne Majalisar ta ware a matsayin ranar yaki da kin addinin musulunci ta duniya.
Iranawani ya bayyana cewa kasashen Turai da daman a da hannu a cikin kokarin raba ayyukan ta’addanci ga addinin musulunci, tare da kafa dokokin wadanda suke bawa wasu damar wulakanta addinai da kona littafansu masu tsarki saboda cusa gaba da kiyyar addinin musulunci da musulmi ga mutanen kasashen su. Da sunan yencin fadin al-barkacin baki.
Daga karshe jakadan ya bukaci kasashen duniya su kakkafa dokoki a kasashensu wadanda zasu bukaci zaman lafiya da mabiya ko wani addini a duniya da kuma kaucewa duk wanda rikicin saboda bambancin addini da kuma nuna wariya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shettima Ya Taya Sarkin Gumel Murna Tare da Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Bunkasa Bangaren Noma
Daga Usman Muhammad Zaria
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yaba da gagarumin cigaba a harkar noma da Gwamna Umar Namadi ya samar cikin shekaru biyu kacal na mulkinsa.
Ya bayyana haka ne a masarautar Gumel cikin Jihar Jigawa, yayin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da Gidauniyar Kashim Shettima ta gina a matsayin wani ɓangare na bikin zagayowar cikar Sarkin Gumel shekaru 45 a kan karaga.
A cewarsa, abin sha’awa ne yadda Gwamna Umar Namadi ya mayar da harkar noma a jihar Jigawa zuwa ta zamani cikin shekaru biyu kacal.
Ya jinjina wa Gwamnan da al’ummar Jihar Jigawa bisa wannan ci gaba mai armashi.
Kashim Shettima ya kara taya Sarkin Gumel, Alhaji Muhammadu Sani, murnar cika shekaru 45 a matsayin Sarkin Gumel, tare da yi masa fatan alkhairi.
Ya tabbatar da ci gaba da jajircewar Gidauniyar Kashim Shettima wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
A jawabinsa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yaba wa Mataimakin Shugaban Kasa bisa kaddamar dadMasallacin.
Ya kuma taya Sarkin Gumel murnar cika shekaru 45 a kan karaga, tare da yi masa fatan alheri.
Shi ma a nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya jinjina wa Mataimakin Shugaban Kasa bisa gina Masallacin Juma’ar.
Namadi ya kuma yaba da jinjinar da VP ya yi kan sauyin da aka samu a harkar noma ta Jigawa, yana mai alkawarin cewa za a cigaba da kara himma a bangaren noma da ma dukkan ababen da za su ciyar da jihar gaba.
Gwamnan ya kara jinjina wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi da sauran manyan baki bisa halartar taro.