’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike
Published: 4th, July 2025 GMT
Ministan Babban Birninn Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa ya yanka wa ’ya’yansa manyan filaye a Abuja, inda ya ce in ma haka ne suna da hakki a matsayinsu na ’yan Najeriya.
Ana dai zargin Wike da ba biyu daga cikin ’ya’yansa fili mai fadin murabba’in hekta 2,082, dayan kuma mai fadin hekta 1,740, wanda aka kiyasta darajarsu ta haura Naira tiriliyan tara.
Da yake zantawa da ’yan jarida a Abuja ranar Alhamis, Wike ya karyata labarin na cewa ya ba ’ya’yan nasa filayen a unguwannin Maitama da Asokoro.
Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC Filato: Mahara sun cire hannun matashi a kan hanyar komawa gida daga jana’izaTo sai dai duk da haka, ya kare batun, inda ya ce a matsayin su na ’yan Najeriya, su ma sun cancanci su mallaki filayen matukar dai an bi ka’ida.
“Alal misali, amma ba wai na amsa haka ba ne, a ce ’ya’yana sun nemi filayen, shin ba su cancanta a ba su ba ne? ko su ’yan Ghana ne? ko kuwa a’a, kawai saboda ni ina minista shi ke nan ba su cancanta ba?,” in ji Wike.
Ministan ya zargi wasu mutane da ya ce ba su da suna daga jihar Adamawa da kitsa zancen domin kawai su bata masa suna.
“Da farko ma ka fara lissafa hekta 2,000 na fili sai ka fada min a ina za ka sami hakan a Asokoro da Maitama. Na san daga jihar Adamawa aka shirya wannan kitimurmurar,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Filaye
এছাড়াও পড়ুন:
Arsenal Ta Sayi Kepa Daga Chelsea
A kakar da ta wuce, Arsenal ta karɓi Neto a aro daga Bournemouth domin taimaka wa Raya, amma yanzu ta yanke shawarar dawo da shi domin ɗaukar Kepa daga Chelsea.
Kepa ya buga wasanni 163 a Chelsea, kuma yana cikin tawagar da ta lashe kofin zakarun Turai, Europa League da kuma kofin ƙungiyoyin duniya (Club World Cup).
Haka kuma, ya shafe shekara guda a aro a Real Madrid, inda ya taimaka musu suka lashe Laliga da Champions League a kakar 2023-24.
Chelsea ta ɗauki Kepa ne a 2018 bayan kasa ɗaukar Thibaut Courtois daga Atletico Madrid da Alisson Becker wanda ya koma Liverpool.
Daga baya kuma ta gane cewa bai cancanci kuɗin da aka kashe a kansa ba, ciki har da albashin fam 190,000 da yake karɓar duk mako.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp