Zargi: ’Yan sanda sun musanta sace tsohon Kwamishinan El-Rufai
Published: 15th, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta ƙaryata zargin da Tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya yi cewa jami’an tsaro sun sace tsohon Kwamishinansa, Jafaru Sani.
El-Rufai ya yi wannan iƙirari ne a shafinsa na sada zumunta cewa an ɗauke tsohon Kwamishinan kamar fursuna ba tare da bin ƙa’idojin doka ba.
Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da KebbiYa yi zargin cewa wata “ƙungiyar masu garkuwa da mutane” da ke da alaƙa da Gwamna Uba Sani ce ke da alhakin ɗauke tsohon Kwamishinan.
Da yake mayar da martani, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana zargin a matsayin ƙarya.
“Babu wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane a cikin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.
“Mu hukuma ce da ke aiki bisa kundin tsarin mulki don tabbatar da doka da oda,” in ji shi.
Ya buƙaci ’yan siyasa su guji yaɗa labaran da ba su da tushe.
“Yi wa jami’an tsaro ƙarya na iya haifar da ruɗani da kuma rage martabarsu. Idan mutum yana da ƙorafi, ya bi hanyar shari’a maimakon yaɗa kalaman da za su tayar da fitina,” a cewarsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Jafaru Sani Tsohon Kwamishina zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp