Aminiya:
2025-11-03@02:15:25 GMT

Lukurawa Sun Kashe Mutane 15 a Sakkwato

Published: 3rd, July 2025 GMT

Wasu ‘yan bindigar da ake zargi Lukurawa ne a wani sabon hari sun kashe mutane sama da 15 a Qaramar Hukumar Tangaza ta jihar Sakkwato, ranar Litinin da ta gabata.

Babban Jami’i a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Qasa(Red Cross) reshen Sakkwato Alhaji Abubakar Ainu ya tabbatar wa Aminiya harin wanda ya yi matuqar tayar da hankalin mutanen yankin ganin an xauki dogon lokaci kafin kawo irin wannan hari mai muni.

Ainu ya ce, “jami’anmu na sa kai sun ziyarci qauyen Kwalajiya na mazabar Magoho a garin Tangaza domin jajantawa da kuma halartar sallah janaza ta muanen da ‘yan bindigar suka kashe sama da 15.  Waxanda suka jikkata an kai su Asibitin Kashi na Wamakko da Asibitin Koyarwa ta Xanfodiyo da na Qwararru a birnin jiha domin karvar magani.”

Ya ce yankin na cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro ta varayin shanu da masu tayar da qayar baya.

“Wannan lamari baya da daxi ko kaxan, dubi yadda aka mayar da wasu mata zawarawa aka mayar da wasu yara marayu domin biyan wata buqata wadda addini bai yarda da ita ba, ina kira ga hukuma ta sake salon yaqar ‘yan bindiga da take yi,” in ji Ainu.

Wani mazauni qauyen Kwalajiya ya ce ‘yan bindigar Lukurawa sun zo a qauyen a daren Lahadi har zuwa Asuba ta ranar Litinin in da suka kashe wasu mutane a harin da suka kai, a lokacin da suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

“Bayan sun kashe mana mutane sun tafi da dabbobi masu yawa, duk da mutanenmu sun yi qoqari amma yawan mutane da makaman da suke xauke da su ya sa suka fi qarfinmu. Har zuwa yanzu ba mu san adadin waxanda aka kai asibiti ba domin suna da yawa, sai dai waxanda suka rasu 15 muka yi wa Sallah.

“Muna kira ga jami’an tsaro su mayar da hankali wurin korar mana waxannan ‘yan bindigar don mu samu zaman lafiya a jiha baki xaya.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan bindigar

এছাড়াও পড়ুন:

‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’

Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.

Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.

Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.

Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.

 

BBC

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure