Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas
Published: 14th, March 2025 GMT
An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas.
Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma kusa da bakin ruwan kogin da ke hanyar jami’ar Legas.
“Tawagar ’yan sandan ruwa da ke aiki a wurin sun gano ta gaɓar ruwan da ke hanyar jami’ar Legas kuma likitocin jami’ar UNILAG sun tabbatar da mutuwarta a gaban rundunar ’yan sanda daga sashin Sabo,” kamar yadda sanarwar a wani ɓangare ta bayyana.
Hundeyin ya ci gaba da cewa, an kai gawar zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin cututtuka masu yaɗuwa da ke yankin Yaba a jihar domin adanawa.
Ya ƙara da cewa “Yan sanda a halin yanzu suna binciken al’amuran da suka shafi mutuwar matar.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696.
Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp