Jami’in Sin: Ba Za A Lamunci Ayyukan ‘Yan Aware Na “Ballewar Taiwan” Ta Ko Wace Hanya Ba
Published: 15th, March 2025 GMT
Wani jami’in yada labarai na babban yankin kasar Sin ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ba za a amince da duk wani mahaluki ko wata runduna da za ta raba yankin Taiwan da kasar Sin ba, kuma babu yadda za a yi a lamunce da ayyukan “ballewar Taiwan” ta ko wace hanya.
Jami’in yada labarun, da ke aiki a ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, Chen Binhua ya kara da cewa, matukar dakarun ‘yan awaren suka kuskura suka bari tura ta kai bango, za a dauki kwararan matakan mayar da martani a kansu.
Chen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yin tir da kalaman jagoran ‘yan awaren Taiwan na baya-bayan nan, Lai Ching-te, wanda ya yi ikirarin cewa bangarori biyu na mashigin Taiwan ba su nuna biyayya ga junansu.
Da yake mayar da martani kan haka, Chen ya jaddada cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya rabuwa da shi ba. Kana bai taba zama kasa ba kuma ba zai zama ba a gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai ta Jigawa ta Kiyasta Naira Biliyan 3 Don Ayyukan Hajjin 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe naira miliyan dubu 3 domin gudanar da aikace-aikacenta a lokacin aikin Hajjin 2026.
Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara a gaban kwamatin harkokin addini na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Alhaji Ahmed Umar Labbo yace hukumar za ta sayi motar daukar marasa lafia wato ambulance domin dawainiya da mahajjatan da za su gamu da rashin lafiya a lokacin hajji a kasa mai tsarki.
Yana mai bayyana cewar za a yi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen kaiwa da komowa yayin aikin hajji.
Sai kama masauki ga ma’aikatan hukumar da ma’aikatan wucin gadi kamar tawagar ma’aikatan lafiya da malamai da ‘yan jarida da ke taimakawa hukumar wajen samun nasarar gudanar da aikin Hajji.
A don haka, Ahmed Labbo ya bukaci maniyyata aikin Hajji da su rika halartar cibiyoyin bita domin koyon ibadar aikin Hajji a aikace bisa doron ilimi.
A nasa jawabin, shugaban kwamatin harkokin addini na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Garki, Alhaji Abdu Ila Muku, ya jaddada kudurin kwamatin na duba sansanin Alhazai.
Abdu Muku yace kwamitin zai kuma duba sauran shirye-shiryen hukumar aikin hajji ta jihar domin tabbatar da samun nasarar aikin hajji mai zuwa.