Haka kuma Wang ya halarci taron ministocin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS da na kasashe kawayensu a wannan rana, inda aka tattauna game da yadda za a karfafa ra’ayin cudanyar bangarori daban daban.

 

Wang ya bayyana cewa, mafitar matsalolin da ake fuskanta a duniya ita ce kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban.

Ya ce bayan da ta habaka mambobinta, ya kamata kungiyar BRICS ta ci gaba yayata manufar yin shawarwari da juna da tabbatar da ci gaban juna da cin moriya tare, da kiyaye muhimman ka’idojin huldar kasa da kasa, da kuma kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban.

 

Wang ya jadadda cewa, amsar da Sin ta bayar game da yakin cinikayya a bayyane take, wato idan an dage kan yakin, ko kadan ba za mu ja da baya ba. Idan an shirya tattaunawa, dole ne mu girmama juna tare da yin zaman daidaito da juna. Ba don hakkinta na kanta ba ne, kasar Sin tana kuma kiyaye muradun bai daya na dukkanin kasashe. Abun da kasar Sin ke kiyayewa ba kawai hadin gwiwar cin moriyar juna ba ne, har ma da ka’idojin kasa da kasa. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

 

Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.

 

Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka October 31, 2025 Daga Birnin Sin Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
  • Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa