Leadership News Hausa:
2025-06-24@06:49:44 GMT

Dogaro Da Kasashen Yamma Ba Zai Tabbatar Da Tsaro A Philippines Ba

Published: 14th, February 2025 GMT

Dogaro Da Kasashen Yamma Ba Zai Tabbatar Da Tsaro A Philippines Ba

Manyan jami’an Philippines sun sake ikirarin shirin sayen makamai masu linzami dake cin matsakaicin zango na Amurka tare da hada su da batun tekun kudancin Sin. Hakika matakin na Philippines ya damka muradun kasar na tsaro a hannun kawayenta na yammacin duniya.

Dabarar Philippines ta dogaro da kasashen yamma ba za ta samar da tsaro a kasar ba, sai ma akasin hakan.

Saboda jibge makamai masu linzamin ya shafi tsarin tsaro na kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN.

A daya bangaren, Philippines na yunkurin cin gajiyar tekun kudancin Sin ta hanyar samun goyon baya daga kasashen dake wajen yankin, inda take ci gaba da takala da tada rikici da ma amfani da batun a matsayin wata dama ta jibge makamai masu linzami na Amurka, wanda yake tura yankin tekun kudancin Sin cikin hadari. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Bio ya maye gurbin Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

Shugaban Ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), inda ya karɓi ragamar shugabancin daga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

An sanar da hakan ne a taron shugabannin ECOWAS karo na 67 da aka gudanar a Abuja.

An kashe matar aure, manomi ya jikkata a wani sabon hari a Kaduna ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa 

Shugaba Tinubu, wanda ya yi wa’adin shugabancin ƙungiyar sau biyu tun daga shekarar 2023, ya bayyana cewa shugabancin ECOWAS babban abu ne a rayuwarsa.

Ya ce: “Yayin da nake miƙa ragamar shugabanci ga abokina kuma ɗan uwana, Shugaba Julius Maada Bio, ina mai gamsuwa da fatan alheri ga makomar Yammacin Afirka.”

Ya ƙara da cewa wajibi ne ƙasashen yankin su haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban dimokuraɗiyya da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

“Mu ƙara inganta haɗin kai, mu mutunta ƙa’idojin diflomasiyya, sannan mu tabbatar da ci gaba wanda zai haɗa kowa da kowa musamman matasa, mata da waɗanda ke cikin mawuyacin hali,” in ji Tinubu.

A jawabinsa na karɓar shugabanci, Shugaba Bio ya gode wa Tinubu bisa jagoranci mai cike da hangen nesa da kyakkyawan fata.

Ya ce: “Shugabancinka a ECOWAS ya nuna jajircewa wajen ƙarfafa tattaunawar yankin, farfaɗo da tattalin arziƙi da wanzar da zaman lafiya.

“Na ji kaina a matsayin mai ɗaukar wannan nauyi domin ci gaba daga inda ka tsaya.”

Shugaba Bio ya bayyana cewa akwai buƙatar ECOWAS ta ƙara dagewa wajen kare dimokuraɗiyya, inganta tsaro da bunƙasa tattalin arziƙi.

“Dole mu sake fasalin ECOWAS ta yadda za ta zama mai gaskiya, inganci da amsa buƙatun al’ummarta,” in ji shi.

Ya kuma bayyana matsalolin da yankin ke fuskanta kamar ta’addanci, taɓarɓarewar siyasa da matsin tattalin arziki.

Ya ce: “Fagen dimokuraɗiyya yana fuskantar ƙalubale a sassa daban-daban na yankin. A wasu ƙasashe, tsarin mulki ya rikiɗe.

“Amma matasa na faɗin Yammacin Afirka na buƙatar ba kawai zaɓe ba, har ma da gaskiya, da ba su damar shiga cikin tafiyar da rayuwar ƙasa.”

Hakazalika, Bio ya ce zai yi jagoranci ECOWAS cikin gaskiya da fifita buƙatun al’umma tare da inganta haɗin kan yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi
  • Gwamnati Ta Bayar Da Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja Duk da Gargaɗin Da Ofishin Jakadancin Amurka Ya Yi
  • Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz
  • Iran: Amurka ta ɗebo ruwan dafa kanta
  • Bio ya maye gurbin Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS
  • Gwamnatin Hong Kong Ta Gudanar Da Bikin Cika Shekaru Biyar Da Kafuwar Dokar Tsaron Kasa Ta Yankin
  • Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?
  • Kungiyar Gamayyar Gidajen Rediyo Da Telabijin Na Kasashen Afirka Ta Ba CMG Kyautar Karramawa
  • Za Mu Tabbatar Da Yin Aiki Da Ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani – Daurawa
  • Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi daraja a Isra’ila