Kar A Mika Wuya Ga “Damisar Takarda”
Published: 30th, April 2025 GMT
To, bayanai a sama sun nuna ra’ayi iri daya na gwamnatocin dimbin kasashe masu tasowa. Ban da haka, wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta Sin CGTN, da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar a kasashe 38, ya nuna cewa, matakan ramuwar gayya da kasar Sin ta dauka kan kasar Amurka suna samun goyon baya tsakanin al’ummun kasashe daban daban, inda a dimbin kasashe masu tasowa da suka hada da Najeriya, da Kenya, da Masar, da Ghana, da Afirka ta Kudu, da Turkiya, matakan kasar Sin suka samu goyon baya daga mutane fiye da kaso 70% da aka gudanar da bincike kansu.
Sai dai kasar Sin ba ta son yakin ciniki, ko da yake tana wakiltar ra’ayi mai adalci na akasarin kasashe. Kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, “Babu mai samun nasara a yakin harajin fito, da na ciniki.” Amma, bisa la’akari da cewa kasar Amurka ce ta ta da yakin ciniki, to, kasar Sin ba za ta taba mika wuyarta ba, kuma ba za ta yi hakuri da matakin cin zarafi ba. Sin ta nanata cewa, idan kasar Amurka na son daidaita al’amarin ta hanyar tattaunawa, to, ya kamata ta “daina barazana da matsin lamba, ta yi tattaunawa bisa tushen daidaito, da mutunta juna, da amfanawa juna.”
Hakika, ban da wadannan abubuwan da aka ambata, don kaddamar da tattaunawa, ana bukatar sanin ya kamata, wanda kasar Amurka ta rasa. Misali, yadda kasar Amurka ta janye jikinta daga dimbin kungiyoyin kasa da kasa, da yarjeniyoyin duniya, da daina samar da tallafi ga sauran kasashe, sun nuna yunkurinta na kaucewa daukar nauyi sakamakon raguwar karfinta a fannin tattalin arziki. Sai dai wannan yanayi mai kunci bai hana ta ci gaba da neman ba da umarni ga sauran kasashe, da cin zarafinsu ba. Ban da haka, mu kan ga yadda shugabannin kasar Amurka suke ba da umarni da gyara shi cikin sauri, da yin karairayi yadda suka ga dama, da wulakanta takwarorinsu na sauran kasashe, da kasa kare bayanan sirrin da suka shafi yaki, wadanda suka nuna gazawarsu wajen aiki. Ma iya cewa, yanzu haka, kasar Amurka tamkar damisar takarda ce, mai ban tsoro amma maras karfi.
Za mu jira lokacin da za a iya komawa teburin shawarwari don tattauna batun kawo karshen yakin ciniki, inda za a jira har zuwa lokacin da kasar Amurka za ta gamu da dimbin matsaloli, ta yadda za ta yi watsi da matakan zalunci, da sake samun sanin ya kamata. Amma yanzu muna iya tabbatar da matakin da ya kamata kasashe masu tasowa su dauka, wato karfafa hadin kansu, maimakon mika wuya ga kasar Amurka, wadda ta kasance tamkar wata “damisar takarda”, da ke neman cin zarafin sauran kasashe, da ta da rikici a duniya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.
Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.
Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp