’Yan Najeriya daga kowane ɓangare daban-daban sun caccaki jam’iyyar APC bisa yanke shawarar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da cewa shekararsa biyu kacal da hawa mulki.

Wasu na ganin matakin ya nuna rashin tausayi da rashin damuwa da halin ƙuncin da al’umma ke ciki.

Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan ƙasar Indonesiya a Saudiyya NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC

Jagororin jam’iyyar APC, gwamnoninta da ’yan majalisa ne suka fito suka nuna goyon bayansu ga Tinubu.

Amma jama’a na ganin hakan na nuna burin ci gaba da riƙe madafun iko ne kawai, ba wai taimakon talakawa ba.

Ra’ayoyi daga sassa daban-daban na Najeriya

A Jihar Legas, Mary Okonkwo, wata ’yar kasuwa ta ce: “Rayuwa na neman gagarar jama’a. Kasuwancina na shirin durƙushewa saboda hauhawar farashi. Kuma suna maganar zaɓe tun yanzu?”

Daga Fatakwal, Daniel Etim, ma’aikacin gwamnati ya ce: “Wannan goyon bayan da suka yi ya yi wuri da yawa, kuma ya nuna rashin mutunta mutane. Albashi ko mako ɗaya ba ya ishar mu.”

A Enugu, ɗalibar jami’a Adaeze Nnaji tambaya ta yi: “Shin wannan ne ladan wahalar da muke sha? Babu wutar lantarki, babu aiki, amma ana yaba wa shugaba wanda bai yi komai ba?”

A Abuja, Rashida Muhammad ta ce: “Tinubu ya ci amanarmu. Komai ya yi tsada kuma muna cikin tsananin wahala. Bai cancanci wa’adi na biyu ba.”

Tafawa Muhammad, wani manomi a Kano ya ce: “Farashin abincin kifi da taki ya ninka sau uku. Aikin gona na ya kusa durƙushewa.”

A Ibadan, Dele Olatunji, malamin makaranta ya ce: “Wadannan goyon baya ba don al’umma ba ne. Sun fi damuwa da kansu.”

Masana siyasa na ganin wannan goyon baya bai dogara da aiki ba, sai dai neman ci gaba da mulki.

Farfesa Hassan Saliu, ya gargaɗi cewa Najeriya na dab da zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

Ya shawarci al’umma da su zauna cikin shiri domin su ɗauki mataki a 2027.

Wani masanin, Dokta Kabiru Sufi, ya ce ’yan siyasa sun fi mayar da hankali kan zaɓe fiye da warware matsalolin da ke addabar ƙasa, kamar tsaro, talauci da yunwa.

Duk da wannan goyon baya da jam’iyyar APC ta nuna, yawancin ‘yan Najeriya na buƙatar shugabanci na gari ne, ba wai alƙawura marasa amfani ba.

A cewar Adaeze Nnaji: “A gyara ƙasa tukunna sai a zo a yi maganar zaɓen 2027.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan Najeriya Goyon Baya Siyasa Takara Watsi Zaɓe

এছাড়াও পড়ুন:

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista

Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.”

 

Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.”

 

Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko, amma yanzu an fara ganin alfanun su, ciki kuwa har da daidaituwar musayar kuɗi, da ƙaruwar kuɗaɗen shiga ga jihohi, da farfaɗowar masana’antun tace mai, da kuma ƙarfafa matsayin kuɗin gwamnati.

 

Yayin da gwamnatin Tinubu take da da cika shekara biyu, ministan ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya suna ganin gagarumin zuba jari da ake yi a harkar ababen more rayuwa, noma, tsaro, da bunƙasa rayuwar ɗan’adam.

 

A cewar sa, an ware naira tiriliyan 2.5 don ayyukan gina manyan hanyoyi a 2025 — adadin da ya fi na kowanne lokaci a tarihin Nijeriya.

 

Ya kuma bayyana ƙirƙirar sababbin ma’aikatu na bunƙasa yankuna da na kiwon dabbobi, domin ƙara bunƙasa arzikin ƙasa da noma da aka yi, da kuma ƙaddamar da shirin lamuni na NELFUND wanda ya taimaka wa ɗaliban Nijeriya sama da 300,000 da kuɗin karatu da gudanar da rayuwar su.

 

Daga cikin sauran muhimman ayyuka da ministan ya lissafa akwai shirin Shugaban Ƙasa na amfani da iskar gas ta CNG a motoci wanda ya jawo zuba jari kai-tsaye na fiye da dalar Amurka miliyan 450; da kafa CreditCorp domin bai wa ‘yan Nijeriya damar samun rance don gina gidajen su da kula da lafiyar su; da kuma ware naira biliyan 200 don tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa, ƙananan sana’o’i (SMEs) da manyan masana’antu.

 

Ya ƙara da cewa: “Yanzu haka Nijeriya ta zama wani gagarumin wurin gine-gine, inda aka kasafta sama da naira tiriliyan 2.5 don gudanar da ayyukan hanyoyi a wannan shekara kaɗai — wanda hakan bai taɓa faruwa ba a tarihin ƙasar nan.

 

“Gwamnati tana haɗa birane ta hanyar manyan ayyuka irin su hanyar Legas zuwa Kalaba da wata hanyar daga Badagry zuwa Sakkwato, da sauran sassa na ƙasa.

 

“Akwai sauran ayyuka da dama da ke gudana yanzu haka. Daga farfaɗowar matatun mai na Fatakwal da Warri, zuwa amincewa da a kashe naira biliyan 80 don sake gina dam ɗin Alau da ke Jihar Borno, zuwa ci gaban aikin gina layin dogo na zamani daga Kano zuwa Kaduna — babu wani yanki na ƙasar da aka bari a baya a cikin wannan babban zuba jari a ababen more rayuwa ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda yanzu ake kira ‘The Road Master.’”

 

Ministan ya kuma nuna wasu alamomin da ke nuna bunƙasar tattalin arziki inda ya ce, “Ma’aunin Canjin Farashin Kayayyaki (CPI) na watan Afrilu 2025, wanda Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta fitar kwanan nan, ya nuna cewa hauhawar farashi ya tsaya a kashi 23.71, wanda an samu raguwar kashi 0.52 daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan bai faru ba sai saboda tsare-tsaren Shugaban Ƙasa, waɗanda yanzu haka sun fara bayyana kuma suna haifar da ɗa mai ido.”

 

Idris ya buƙaci ƙwararrun masanan hulɗar jama’a da su taka rawar gani wajen gina da kuma nuna sabuwar martabar tattalin arzikin Nijeriya ga duniya.

 

“Nijeriya tana bunƙasa!” inji shi. “Nijeriya ta jawo fiye da dalar Amurka biliyan 50 na sababbin hannun jari kai-tsaye daga ƙasashen waje, kuɗin da ‘yan Nijeriya suke turowa daga ƙetare sun kai dala biliyan 21.9, kuma masana’antar finafinai (Nollywood) ta bayar da gudunmawar fiye da naira biliyan 730 ga haɓakar tattalin arziki (GDP).

 

“Waɗannan ba ƙididdiga ba ne kawai — su ne labarai da suke buƙatar a bada su ta hanya mai kyau, bisa ƙwarewa, kuma cikin ƙaunar ƙasa.”

 

Idris ya jaddada cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da inganta saƙonnin ƙasa ta hanyar sabon tsarin sadarwa na ƙasa mai suna National Strategic Communication Framework (NSCF).

 

Ya kuma taya Shugaban Hukumar NIPR, Dakta Ike Neliaku, murna bisa zaɓen sa a matsayin Wakilin Lardi na Musamman (Regional Delegate-at-Large) na ƙungiyar Global Alliance for PR and Communication Management.

 

Ya ce: “Ina taya ka murna, ya Shugaban mu, bisa wannan gagarumar nasara. A ƙarƙashin jagorancin ka, aikin hulɗar jama’a ya samu ƙarin daraja sosai a gida da wajen Nijeriya.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu
  • An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya
  • ‘Aikin Yan Uba Ne’ — Yahaya Bello Ya Karyata Zargin Sha’awar Takarar Shugaban Kasa A 2027
  • Jam’iyyar APC A Najeriya Ta Tabbatar Da Tinubu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar A Shekara Ta 2027
  • Ba mu tilasta wa kowa ya koma APC ba – Tinubu
  • Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 
  • Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A Zaɓen 2027 
  • Shirye-shiryen Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista
  • Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista