An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya
Published: 23rd, May 2025 GMT
Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya, NRC ta tabbatar da kama ma’aikacinta mai suna Gift Eseeli, mai shekara 38, bisa zargin satar waya a Rafa Yard da ke kan hanyar Warri-Itakpe a harabar tashar jirgin ƙasa (WITS) Jihar Delta.
Jami’an rundunar Man O’war na shiyyar Railway Command ne suka kama ma’aikacin.
A cewar mai magana da yawun hukumar ta NRC, Callistus Unyimadu, binciken farko na nuni da cewa an cire dogayen wayoyin da suke ba da sigina masu sulke mai tsayin 50mm daga na’urorin gefen titin kafin jami’an ‘yan banga ƙarƙashin jagorancin Mista williams Agiake su cafke wanda ake zargin.
2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan ƙasar Indonesiya a SaudiyyaAn gano kayayyakin da aka sace, kuma an miƙa su ga rundunar ’yan sandan Najeriya inda ta fara gudanar da cikakken bincike.
Manajan Darakta na NRC Dakta kayode Opeifa, a cikin sanarwar ya yi Allah wadai da faruwar lamarin tare da jaddada cewa waɗanda aka samu da laifin lalata dukiyar ƙasa za su fuskanci fushin doka.
“Kadarorin titin jirgin ƙasa mallakin kadarorin ƙasar Najeriya ne. Ayyukan ɓarna na barazana ga lafiyar fasinjoji tare da yin zagon ƙasa ga ayyukan muradun sabuwar Najeriya na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
Ya ce, Hukumar ta NRC za ta gurfanar da duk wani mutum ko ƙungiya ciki har da ma’aikatan da aka samu da laifin yin ɓarna ba tare da ƙetare iyaka ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Asiwaju Bola Tinubu Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya Jihar Kogi
এছাড়াও পড়ুন:
An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta sanar da samun nasarar kuɓutar da wata mace mai shekara 22 da aka yi garkuwa da ita tare da kama wasu mutum biyu.
An kama mutum biyun ne da ake zargi da alaƙa da wani mummunan hari a ƙauyen Tashan Randa da ke ƙaramar hukumar Fika.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce samamen da aka gudanar tare da haɗin gwiwar mafarautan yankin, ya nuna wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarin da rundunar take yi na yaƙi da rashin tsaro a jihar.
An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Dangote ya sake rage farashin man feturSanarwar ta ce, a ranar 6 ga Mayu, 2025 da misalin ƙarfe 5:58 na yamma, wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki gidan Maikudi da ke ƙauyen Tashan Randa, inda suka yi awon gaba da ’yarsa tare da raunata wata yarinya maƙwabciyarta da harbin bindiga.
Sanarwar ta ƙara da cewa, jami’an rundunar sun gaggauta gudanar da bincike, inda suka yi amfani da buƙatar kuɗin fansa da ake nema ₦5,000,000 domin gano masu garkuwa da mutanen.
“An kama wasu mutane biyu, Waiti Bello mai shekara 30 daga ƙauyen Jangalawaje da Idrissa Adamu mai shekara 35 na ƙauyen Biriri, ƙaramar hukumar Gujba, dukkansu sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa, kuma suna taimakawa wajen gudanar da bincike.
“An samu nasarar gano bindigar toka guda ɗaya da babur da aka yi amfani da su wajen kai harin.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Yobe, CP Emmanuel Ado, ya tabbatar da ƙudurin rundunar na kawar da munanan laifuka.” Muna ci gaba da jajircewa wajen kare al’ummarmu.
Wannan nasarar ta nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da ’yan ƙasa,” inji shi, inda ya buƙaci mazauna yankin da su bayar da rahoton abubuwan da ake zargi ga rundunar don magance lamurra kafin su kasance. Cewar CP Emmanuel.