Amurka Tana Takurawa JMI Don Biyan Bukatun HKI Na Ta Dakatar Da Shirinta Na Nukliya
Published: 23rd, May 2025 GMT
Gwamnatin kasar Amurka tana takurawa JMI ne don ta dakatar da shirinta na makamashin nukliya. Don haka ne Amurka take barazana ga Iran a kan cewa idan bata amince a cimma yarjeniya da ita a kan shirinta na makamashin Nukliya ba to ba abinda ya rage sai zabinb soje don wargwaz cibiyotyin makamashin nukliya na kasar Iran.
Wannan bukatar itace HKI ta yi ta nanatawa a MDD a kuma duk inda jami’an gwamnatinta suka yi jwabi shekara da shekaru. A halin yanzu Amurka na bin wannan Shirin sau da kafa. Wata majiya ta shaidawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa, a zagayen tattaunawa har 4 wadanda kasashen biyu suka gudanar za’a fahinci cewa Amurka tana bukata a wajen Amurka fiye da abunda ta gabatar a zaman taro na farko, na biyu na uku da na hudu da suka gabata.
Sai zai don tsoron kada ta kori Iran tun ba’a je ko in aba, taki ta kawo wadannan al-amura, said ai ta bayyana su a kafafen yada labarai.
Manufar tattaunawar dai kamar yadda Amurka ta bayyana itace hana Iran mallakar makaman Nukliya. Amma sai ta bayyana bas hi bane bayan zagaye na 4, manufar itace hana Iran tace makamacin Uranium kwatakwata. Abbas Argchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya manufar ta na shiga tattaunawa ba kai tsaye ba da Amurka it ace ganin an dauke mata takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasa. Amma a tattaunawar da suka gabata Amurka bata ma kawo batun ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce: Amurka Ba Ta Fadan Hakikanin Abubuwan Da Aka Tattauna A Zamanta Iran
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Matsayin Amurka a cikin ɗakin tattaunawa da Iran ya bambanta da abin da suke shelantawa a waje
Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Kalamai da matsayar da jami’an Amurka suka dauka a cikin dakin tattaunawa da Iran suna shan bamban a fili da abin da suke bayyanawa a bainar jama’a, yana mai cewa wannan sabani yana dakushe kwarin gwiwar bangaren Iran da kuma yin barazana ga makomar shawarwarin.
A wata hira da ya yi da mujallar Der Spiegel ta Jamus, Takht-Ravanchi ya bayyana kin amincewar da Iran ta yi da bukatar “samar da sifili na Uranium da take sarrafawa”, yana mai jaddada cewa inganta sinadarin Uranium don manufar zaman lafiya wani muhimmin bangare ne na shirin makamashin nukiliyar Iran kuma wani hakki ne da ba za a iya tattaunawa kansa ba.
Yana mai jaddada cewa: “Idan har Amurka ta nace da batun dakatar da duk wani abu da ake yi na inganta sinadarin Uranium, to lallai tattaunawar da ake yi ba za ta kai ga gaci ba,” Ya kara da cewa: Tace sinadarin Uranium wani babban nasara ce ta kasa, kuma Iran ba za ta yi watsi da shi ba, yana mai jaddada cewa har yanzu ba a sanya batun wa’adin (kamar shekaru 25) kan teburin tattaunawa ba.