HausaTv:
2025-07-31@13:57:36 GMT

Afirka ta Kudu: Ba Za Mu Janye Kararmu Kan Isra’ila A Kotun ICJ Ba

Published: 14th, February 2025 GMT

Afirka ta Kudu ta yi alkawarin ci gaba da shari’ar kisan kiyashi da ta shigar a gaban kotun ICJ a kan Isr’ila,  duk da umurnin da Donald Trump ya bayar na katse taimakon da Amurka ke ba kasar Afirka ta Kudu saboda matakin da ta dauka kan babbar kawar Amurka.

“Babu wata dama” kan janye karar ta  ICJ, ba tare da la’akari da duk wata barazana ko mataki da Trump zai dauka ba, a cewar ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu Ronald Lamola, wanda ya kara da cewa, “Tsayawa a kan ka’idojinmu wani lokaci yana da sakamako, amma mun tsaya tsayin daka kan wannan batu, ganin cewa yana da muhimmanci ga duniya, da kuma bin doka da ka’ida.

Dokar da Trump ya sanya wa hannu ta dakatar da ba da taimako ga Afirka ta Kudu, ya kuma yi alkawarin ci gaba da daukar wasu matakan domin takura kasar Afirka ta kudu kan matakin shigar da kara da ta dauka a kan Isra’ila game da batun yakin Gaza.

Afirka ta Kudu ta gabatar da karar kisan kiyashi kan “Isra’ila” a karshen shekara ta 2023 zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, inda ta bukaci kotun kasa da kasa da ta dauki matakai kan mahukuntan Isra’ila saboda karya yarjejeniyar kisan kare dangi ta Majalisar Dinkin Duniya.

Ireland a hukumance ta shiga cikin shari’ar Afirka ta Kudu a watan Disamba 2024, kuma jim kadan bayan haka, Cuba ta sanar da aniyar ta na shiga cikin lamarin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya shimfiɗa wa Isra’ila wasu jerin sharuɗan da ya ce idan ba ta cika ba, Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu.

A ranar Talata ne Mista Starmer ya ce idan har Isra’ila ba ta cika waɗannan sharuɗa ba zuwa watan Satumba Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu.

Sharuɗɗan da firaministan ya gindaya sun haɗa da:

Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar sake shigar da agaji Gaza Amincewa da yuarjejeniyar zaman lafiya na dogon lokaci wanda zai ”samar da ƙasashe biyu” Tabbatar da cewa ba za a ci gaba da ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ba

Haka kuma Keir Starmer ya kuma sake jaddada buƙatun da Birtaniya ke da su kan Hamas da suka haɗa da:

Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Sakin duka sauran Isra’ilawan da take riƙe da su Amincewa ba za ta saka hannu a tafiyar da gwamnatin Gaza ba Miƙa duka makamanta

BBC/Hausa

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Sojojin Sahayoniya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza
  • Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga
  • Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000
  • Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka
  • Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
  • Birtaniya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Mutane 33 A Zamfara
  • Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine
  • Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci
  • Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki
  • Shugaban Kasar Masar Ya Roki Trump Ya Kawo Karshen Yaki A Gaza