Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Matsayin Amurka a cikin ɗakin tattaunawa da Iran ya bambanta da abin da suke shelantawa a waje

Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Kalamai da matsayar da jami’an Amurka suka dauka a cikin dakin tattaunawa da Iran suna shan bamban a fili da abin da suke bayyanawa a bainar jama’a, yana mai cewa wannan sabani yana dakushe kwarin gwiwar bangaren Iran da kuma yin barazana ga makomar shawarwarin.

A wata hira da ya yi da mujallar Der Spiegel ta Jamus, Takht-Ravanchi ya bayyana kin amincewar da Iran ta yi da bukatar “samar da sifili na Uranium da take sarrafawa”, yana mai jaddada cewa inganta sinadarin Uranium don manufar zaman lafiya wani muhimmin bangare ne na shirin makamashin nukiliyar Iran kuma wani hakki ne da ba za a iya tattaunawa kansa ba.

Yana mai jaddada cewa: “Idan har Amurka ta nace da batun dakatar da duk wani abu da ake yi na inganta sinadarin Uranium, to lallai tattaunawar da ake yi ba za ta kai ga gaci ba,” Ya kara da cewa: Tace sinadarin Uranium wani babban nasara ce ta kasa, kuma Iran ba za ta yi watsi da shi ba, yana mai jaddada cewa har yanzu ba a sanya batun wa’adin (kamar shekaru 25) kan teburin tattaunawa ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Ce; Ba Ta Gaggawar Neman Kulla Alaka Da Kasar Siriya

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda alaka da Iran za ta iya taimakawa al’ummar Siriya, a shirye mahukuntan Iran su amsa bukatar ta.”

A wata hira da tashar talabijin ta Al Sharq, Araqchi ya jaddada dimbin damammaki, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gaske take yi wajen kulla kyakkyawar huldar makwabtaka da yankin da ke kewaye, kuma Iran ta bi ta wannan hanya.”

Ya kara da cewa: “Iran ta kulla alaka mai kyau ta fuskar siyasa, tattalin arziki da al’adu tare da dukkan makwabtanta da kasashen da ke kewaye, Iran makwabciya ce da Siriya kuma kasashen biyu suna zaune a yanki guda tsawon dubban shekaru.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kara Haske kan Batun Inganta Sinadarin Uranium Da Zamanta Da Amurka
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Ce; Ba Ta Gaggawar Neman Kulla Alaka Da Kasar Siriya
  • Iran Ta Gamsu Da Lokaci Da Wurin Da Za A Gudanar Da Shawarwarinta Da Amurka Zagaye Na Biyar
  • Araghchi: Iran ba za ta tattauna kan batun inganta sinadarin Uranium din ta ba
  • Za’a Gudanar Da Tattaunawa Zagaye Na 5 Tsakanin Amurka Da Iran A Ranar 23-Afrilu A Roma
  • An Tattauna Hanyar Zamanantar Da Kasa A Dandalin Tattaunawa Na Masanan Sin Da Afirka
  • Sharhin Bayan Labarai: Iran Zata Ci Gaba Da Tashe Uranium Tare Da Yarjeniya Ko Babu Ita
  • Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Ce; Gwamnatin Siriya Zata Iya Rugujewa Cikin ‘Yan Makonni
  • Iran ba ta jiran izinin kowa kan tace uranium, Dole ne Amurka ta daina maganar banza_Jagora