SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)
Published: 23rd, May 2025 GMT
A gefe guda kuma, al’ummar yankin ne suka sadaukar da gonakinsu, domin amfanin jama’a wajen gina sansanin FCDA. An cimma yarjejeniya cewa; a karshen amfani da filin, za a mayar da shi ga al’umma. Malam Ladan, ya dage har aka tabbatar da wannan yarjejeniya a rubuce kuma Marigayi Abubakar Koko, Sakataren FCDA, ya sa hannu don kada a samu sabanin tarihi.
Amma duk da haka, ba a mika kadarar ba har zuwa shekarar 1987, bayan fafutukar kwato ta tsawon lokaci. Daga bisani kuma, aka mika ta ga kungiyar tsoffin sojoji ta Nijeriya (Nigerian Legion), bayan sun nemi haka. Abin bakin ciki, gwamnatin tarayya ta kara lissafa filin a matsayin daya daga cikin kadarorinta da za a sayar a zamanin mulkin Obasanjo.
Da ba a gano takardun da Marigayi Koko ya sa hannu a kansu daga cikin tsohuwar ajiyar Jihar Neja ba, da an kwace filin. Wannan kuwa sakamakon hangen nesa ne na Malam Ladan.
Bayan dawo da ikon filin a karo na biyu a ranar 30 ga Oktoba, 2007, al’umma suka mika filin ga Gwamnatin Jihar Neja, domin bai wa Jami’ar IBB ta jihar damar kafa reshe a Suleja. Amma fiye da shekara 17 da yin haka, Gwamnatin Neja ta kasa ware ko sisin kwabo don fara gina wannan reshe.
Abin takaici, tun bayan kirkiro Jihar Neja a 1975, babu wata jami’ar gaba da sakandire da gwamnatin jiha ko ta tarayya ta kafa a Masarautar Suleja, duk da koke-koke da dama, har ma da kiran da dan Majalisar Suleja ya yi kwanan nan a gaban majalisar jihar. Wasu sassan na jihar har suna alfahari da dama daga cikin irin wadannan cibiyoyi. Har da shirin kafa makarantar koyon aikin jinya a tsohon wurin makarantar jinya ta FCT a sansanin FCDA ya zama kawai na cin fuska ne kawai. Hakan na faruwa duk da cewa; akwai Cibiyar Lafiya ta Tarayya da aka ware domin Suleja, amma aka karkatar da ita zuwa wani gari a cikin jihar.
Yankin Masarautar Suleja, shi ne mafi tasiri a fannin tattalin arziki a Jihar Neja, saboda kusancinsa da babban birnin tarayya. Gwamnatin Jihar Neja, na ci gaba da cin moriyar hakan ta hanyar tara haraji masu tarin yawa kamar PAYE, kudin filaye da kadarori da sauran haraji. Masarautar Suleja ita kadai na ba da akalla kashi 40 cikin 100 na kudaden da jihar ke samu daga cikin gida. Kudaden harajin da ake tarawa daga Karamar Hukumar Suleja, sun fi na kowace karamar hukuma a jihar. A kwana-kwanan nan, gwamnan ya bayyana haka.
Amma fa, idan aka kwatanta da wasu garuruwa a cikin jihar, ingancin titin da ake ginawa a cikin birnin Suleja, bai kai kima ba ko kadan. Daga Maje zuwa Madalla, ana iya cewa kwangila ce ta biliyoyin Nairori. Amma kuma, babu wani allon kwangila da ke bayyana sunan dan kwangilar ko hukumar da ke sa ido. Wannan yana nuna irin gazawar da ake da ita wajen gaskiya da rikon amana cikin mulki.
Jama’ar Suleja da masu kaunar garin, ba su da wani zabin da ya wuce su saka a ransu cewa; wata boyayyar makarkashiya ce aka shirya, don rage kudin aikin domin amfanuwar wasu. Wannan kuwa, wata shaida ce ta yadda ake yi wa wanda ke kawo riba wulakanci. Abin takaici ne a ce garin da ke bayar da kudaden shiga ya zama wanda aka watsar da shi a fannin gine-gine da walwalar jama’a.
Za a ci gaba In Shaa Allah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Kai Wa Filin Jirgin Saman “Ben Gorion” Hari Sau Biyu A Yau Alhamis
A karo na biyu sojojin kasar Yemen sun sanar da kai hari akan filin saukar jirgin sama na “Ben Gorion” a matsayin ci gaba da taimakawa Falasdinawa da sojojin HKI suke yi wa kisan kiyashi.
Sanarwar ta sojojin na Yemen ta kuma ce; Makami mai linzamin da su ka harba, wanda ya fi sauti sauri ne, kuma ya sauka a inda aka harba shi, wato filin jiragen sama na Yafa dake karkashin mamaya, da ake kira da “Ben Gorion.”
Harin ya tilastawa miliyoyin ‘yan sahayoniya guduwa zuwa Mabuya sanadiyyar gittawar makami mai linzamin da aka harbo daga kasar Yemen. Haka nan kuma an dakatar da zirga-zirgar jirage a filin na Ben Gorion.
Da safiyar yau ma dai kakakin sojan kasar ta Yemen Janar Yahya Sari, ya sanar da harba makami mai linzamin zuwa Tel Aviv, da kuma jiragen sama marasa matuki zuwa tashar jiragen ruwa na Haifa.
Janar Sari ya tabbatar da cewa sojojin na Yemen za su ci gaba da kai hare-haren nasu akan HKI har zuwa lokacin da za a dakatar da yakin Gaza.