Limamin Masallacin Jumma’a A Nan Tehran Ya Yi Magana Dangane Da Kwatar Garin Khurramshar Daga Sojojin Sadam
Published: 23rd, May 2025 GMT
Mataimakin limamin Jumma’a a nan Tehran Sheikh kum Hujjatul Islam Kazen Sadiki bayan yayio Magana a kan al-amuran tsaron All..da kuma yadda bayin All..da kuma shidanun mutane zasu mutu da kuma yadda sakamakon ko wannansu a gaban All…/ Ya kuma ya gamanar fatahin garin KharramShahr dake kudancin kasar Iran kuma kan iyaka da kasar Iran, wanda dakarun kare juyin juya halin musulunci tare da sauran sojoji da mayakan sa kai suka kwace wannan garin daga hannun sojojin Sdam Hussain a rana irin ta yau wato 2 ga watan Khordod.
Banda haka lamamin yana Magana kan littafan da aka buga dangane da wannan gagarumin fatahin da mutanen Iran suka sami a kan wannan garin. Wanda kuma daga wannan nasarar ne ta ci gaba da samun nasara har aka kawo karshen yakin a shekara 1988M.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
Harkokin siyasa na Kudancin Kaduna ya dauki wani salo yayin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar tarayya, Hon. Dan Amos, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP, yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya hada kai da gwamnatocin jiha da na tarayya don cigaban yankin.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kafanchan kafin karbar sa a hukumance tare da Sanata Marshall Katung, Amos ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da shugabannin al’umma, kungiyoyin addini, kwararru da kuma sarakunan gargajiya a fadin mazabarsa.
Ya ce jam’iyyar PDP, wacce a da take da karfi sosai a Kaduna, ta ragu saboda rikice-rikicen cikin gida da suka dade suna faruwa, wanda hakan ya janyo ficewar mambobi da kuma rasa goyon bayan talakawa a fadin kasa.
“Mun dauki lokaci muna tattaunawa da mutane a matakai daban-daban – daga tsarin jam’iyya zuwa kungiyoyin addini da na kwararru – kuma abin da muka cimma shine, don amfanin jama’armu, ya dace mu nemi wata madogara ta daban,”
“Ya zama sauki mu shiga APC saboda muna ganin irin kokarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani ke yi wajen hada yankin Kudancin Kaduna cikin shirin cigaba da ci gaba da kasa.” in ji Amos.
Dan majalisar ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa nadin ɗan asalin yankin, Janar Christopher Musa, a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS) da kuma amincewa da a kafa Jami’ar Kimiyyar Aiki ta Tarayya da Asibitin Tarayya (Federal Medical Centre) a yankin.
Ya kuma gode wa Gwamna Uba Sani saboda gudanar da mulki cikin hadin kai, gina ababen more rayuwa, da bude kofa ga kowa, wanda ya ce ya karfafa zumunci da bai wa kowane bangare na jihar damar shiga.
“Shugaban kasa da gwamna suna nuna shugabanci na hada kan jama’a. Wannan ya sa muka ga dacewar mu hade da su domin mu samu karin cigaba a yankinmu,” in ji Amos.
Amos ya karyata jita-jitar cewa ya koma APC don son kai ko muradin siyasa, yana mai cewa wannan mataki ne na Allah da kuma na amfanin jama’ar Kudancin Kaduna.
“Ba don bukatar kaina ba ne, amma don mu tabbatar da yankinmu ya ci gajiyar dimokuradiyya. Ina da yakinin cewa tarihi zai tuna da mu bisa wannan mataki na jarumta da muka dauka,” ya kara da cewa.
Dan majalisar, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Ayyukan Majalisa, ya tabbatar wa mazaunar mazabarsa cewa komawarsa APC ba za ta canza manufarsa ta kyakkyawan wakilci ba, yana mai cewa ya shiga jam’iyyar mai mulki ne don kara daraja, ba don kawo rarrabuwar kawuna ba.
Ya bayyana fatan cewa da hadin kai tsakanin jama’a da gwamnati, Kudancin Kaduna zai ci gaba da samun cigaba a bangaren ababen more rayuwa, ilimi, da tsaro.
An shirya taron karbar Amos, Sanata Katung, da sauran wadanda suka koma daga PDP zuwa APC a ranar 1 ga Nuwamba a Kafanchan, kuma manyan baki da ake sa ran halarta sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, da kuma shugabannin jam’iyyar APC daga fadin kasar nan.
Radio Nigeria ta ruwaito cewa wannan sauyin jam’iyya ya nuna babban sauyi a siyasar jihar Kaduna, wanda ya kawo karshen rinjayen PDP da ta yi sama da shekaru 25 a Kudancin jihar.
Daniel Karlmax