‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu
Published: 23rd, May 2025 GMT
An dai fara goyon bayan tazarcen Tinubu a wurin taron lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa a 2027.
Barau ya ce, “A bayyane yake a 2027, za mu sami gagarumar nasara, In Sha Allah. Don haka, mu ci gaba da hanyar da muke kai. Mu hada kai da juna, mu yi aiki tare da shugaban kasa, mu yi aiki tare da kowa, mu hada kai a tsakaninmu don samun nasarar da ake bukata.
Sanata Barau ya ci gaba da cewa sauya shekan wasu shugabannin jam’iyyun adawa zuwa APC ya kasance sakamakon aikin Shugaba Tinubu a cikin shekaru biyu kawai da ya shafe a kan karagar mulkin Nijeriya.
Kazalika, Ganduje ya ce Shugaba Tinubu na da kishin ci gaban Arewa Maso Yamma da dukkan yankin Arewa da ma Nijeriya gaba daya, don haka ya cancanci wa’adin mulki na biyu.
Ya ce yi matukar yin kokari ta hanyar wasu ayyukan da gwamnatisa ta bijiro da su, tun daga kan samar da kayayyakin more rayuwa har zuwa bunkasa bangaren noma a yankin Arewa.
Ganduje ya jaddada cewa kafa ma’aikatar bunkasa yankin Arewa Maso Yamma alama ce a fili na cewa shugaban kasa yana son yankin Arewa Maso Yamma.
Haka kuma, Gwamna Uba Sani ya ce yankin Arewaci Maso Yammaci ya bunkasa a karkashin jagorancin Shugaban kasa Tinubu.
“Shugaba Tinubu ya karbi iko ne lokacin da al’amuran kasarmu suka kasance mafi munin kalubale a tarihinta,” in ji shi.
Ya yaba da canje-canje masu amfani na Tinubu, yana cewa, “Shugaban ba ya jin tsoron yanke shawara masu wahala. ‘Yan Nijeriya ma sun fara fahimtar cewa Mai Girma Shugaba yana da kyawawan manufofi ga kasarmu.”
A nasa jawabin, shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce ficewar wasu daga jam’iyyun adawa zuwa APC ya nuna karuwar yarda da ‘yan Nijeriya ke nuna wa jam’iyyar da shugabancinta, amma ya jaddada cewa jam’iyyar dole ne ta karfafa yawan masu goyon baya tun daga mataki na kasa.
A cikin martaninsa, shugaban jam’iyyar ADC, Dakta Ralphs Okey Nwosu, ya ce Tinubu bai cancanci yin tazarce ba.
Nwosu, a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai, ya ce idan aka duba matsayin shugaban kasa bisa kashi, yana iya samun kashi 10 kacal cikin dari sakamakon rashin tsinana abun kirki na shugabancin kasar nan.
Da yake magana kan goyon bayan shugaban kasa daga masu ruwa da tsaki na APC a Kaduna, Nwosu ya ce ‘yan adawa ne kadai za su iya ceto kasar nan, yana mai cewa idan har APC ta ci gaba da mulki a 2027, mutane da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya za su mutu da yunwa.
Amma jam’iyyar SDP ta ce ‘yan Nijeriya za su tantance wane ne zai yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027 idan lokaci ya yi.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Araba Rufus Aiyenigba, ya shaida hakan, inda ya ce, “Mutanen Nijeriya ne za su tantance wanda zai zama shugaban kasan Nijeriya a 2027, ba shugabannin APC ba,” in ji Aiyenigba.
Sakataren yada labarai na NNPP, Ladipo Johnson, ya ce goyon baya daga cikin gida na jam’iyya na da karancin tasiri wajen gwada gwazon gwamnati.
Shi kuwa wani mamba na kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP, Tim Osadolor ya ce goyon bayan Shugaba Tinubu ba zai haifar da komai ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Arewa Maso Yamma yankin Arewa yan Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin HKI Sun Bude Wuta Kan Jami’an Diblomasiyyar Wadanda Suka Je Jenin
Sojojin HKI sun bude wuta nag aske kan jami’an diblomasiyya na wasu kasashen Turai wadanda suke kokarin shiga sansanin yan gudun hijira na Jenin don galin yadda rayuwa take tafiya a cikinsa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jamilan diblomasiyya wadanda suke ziyarar sansanin yan gudun hijiran a yau Laraba dai sun hada da jakadun kasashen Austria, Brazil, Bulgaria, Canada, Chile, China, Masar, Faransa, India, Japan, Jordan, Lithuania, Mexico Morocco, Poland, Portugal, Romania, Rasha, Sri Lanka, Spain, Turkey, tarayyar Turai (EU), da kuma Burtaniya. Tare da su akwai wakilai daga wasu kasashen duniya da kuma yan jarida.
Ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin Falasdinawa ne ta shiryawa wadannan kasashen ziyara zuwa wannan yankin na yamma da kogin Jordan don ganewa idanunsa yadda HKI ta maida rayuwan falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye.
Ma’aikatar ta aiwatar da irin wannan ziyarar zuwa sansanin yan gudun hijira na Tulkaram da ke yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye.
A wasu hotunan bidiyo da aka nuna, an ga yadda wasu jami’an diblomasiyya suke nuna fushinsu da yadda sojojin yahudawan sukabude masu wuta.