Iran: Inda Makiya Kasar Sun San Cewa Zasu Sami Nasara A Kan Iran A Yaki Da Tuni Sunn Farmata Da Yaki
Published: 23rd, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa da Amurka da HKI sun san cewa zasu sami nasara a kan kasar Iran da yaki da tuni sun fadawa kasar sun kuma mamayeta.
Amma saboda wannan tsoron ne suka zabi tattaunawa da ita a kan shirinta na makamshin nukliya. Sannan Shirin makamacin nikliya ma daya ne kacal daga matsalolin da ke tsakanin Iran da HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka.
Arachi ya bayyana cewa kasashen yamma musamman Amurka sun dorawa kasar takunkuman tattalin arziki masu yawa, amma mafi muhimmanci daga cikinsu su ne na makamashin nukliya, don Shirin makamashin nukliyar kasar ne Amurka ta dora mata takunkuman hana saida man fetur ta kuma rana bankunan kasar Iran da Swift, wato aikin da sauran bankunan a duniya. Kuma su ne suka fi cutar da tattalin arzikin kasar. Daga karshe Aragchi ya bayyana cewa in akwai hanyar cira wadannan takunkuman Iran ba zata yi jiunkiri ba, amma kuma tana rayuwa da takunkuman tun shekar ta 2018. Amurka ta kasa cimma manufarta don wadannan takunkuman wanda kuma shine takurawa mutane su tashi su kifar da gwamnatin JMI wanda bai faru ba kuma ba zai faruba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Ce; Ba Ta Gaggawar Neman Kulla Alaka Da Kasar Siriya
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda alaka da Iran za ta iya taimakawa al’ummar Siriya, a shirye mahukuntan Iran su amsa bukatar ta.”
A wata hira da tashar talabijin ta Al Sharq, Araqchi ya jaddada dimbin damammaki, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gaske take yi wajen kulla kyakkyawar huldar makwabtaka da yankin da ke kewaye, kuma Iran ta bi ta wannan hanya.”
Ya kara da cewa: “Iran ta kulla alaka mai kyau ta fuskar siyasa, tattalin arziki da al’adu tare da dukkan makwabtanta da kasashen da ke kewaye, Iran makwabciya ce da Siriya kuma kasashen biyu suna zaune a yanki guda tsawon dubban shekaru.