Allah Ya Isa: Shugaban PDP Damagun ya musanta zargin yi wa APC aiki
Published: 23rd, May 2025 GMT
Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Umar Iliya Damagun, ya yi Allah Ya isa ga masu zargin da yi wa jam’iyya mai mulki, APC, aiki.
Wasu masu ruwa da tsaki a PDP na zargin cewa Damagun da yi wa jam’iyyar zagon ƙasa APC, shi ya sa yake rura wutar rikicin cikin gida da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a PDP.
Amma a yayin wata hira da ya yi da BBC, Damagun ya yi fatali da zargin, yana mai cewa Allah Zai saka masa tsakaninsa da masu yi masa wannan ƙazafi.
“Allah Ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan ƙazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a,” in ji shugaban na PDP, wanda ake zargi da zama ɗan-amshin-shatan APC.
Ya ce, “Da zan shiga Jam’iyyar APC, da tun lokacin Buhari na shiga,” in ji shugaban na PDP, wanda ake zargi da zama ɗan-amshin-shatan APC.
“Tun da na shiga jam’iyyar PDP a 1999 ban taɓa sauya sheƙa ba. Dole wanda ba ya so na zai nemi yadda zai yaɓa min zargi don ya samu biyan buƙatarsa. Na ce ma na je na yi mitin da Tinubu, a Ingila, wannan duk masu yin wannan na bar su da Allah,” in ji shi.
Dangantaka da Wike da sauya sheƙar mambobiDangane da zargin sa da kusanci da kuma alaƙa da Ministan Abuja kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, da kuma yi wa PDP zagon-ƙasa, Damagun ya mayar da martani da cewa: “Duk masu zargin yau ina alaƙa da Ministan Abuja, kan na san shi ko na yi alaƙa da shi, da yawansu sun yi alaƙa da shi. Ni dai laifina guda ɗaya a nan shi ne ban yardar musu yadda suke so su yi da shi ba.”
Game da yadda wasu manyan jaga-jigan jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC, Damagun ya ce sauya sheƙar ta ba wa jam’iyyar PDP takaici, duk da cewa babu laifin da aka yi wa masu ficewan.
Ya ce amma duk da haka jam’iyyar tana ƙoƙarin dinke ɓarakar da ta kunno kai a cikinta.
“Yawanci al’amari yana tasowa idan mutum abubuwa suka faru zai nemi dalili da zai ce shi ya tafi,” kamar yadda ya bayyana
“Babu wanda zai ce PDP ta masa laifi”Damagun ya bugi ƙirji da cewa duk waɗanda suka sauya sheƙa, babu wanda zai iya fitowa ya ce jam’iyyar ta yi masa wani laifi: “Sai dai ma ta yi musu riga ta yi musu wando.”
Ya jaddada cewa PDP ba ta da wata matsala da har ta kai a yi ɓangarori a cikinta.
Amma ya tabbatar da cewa suna da matsalolin cikin gida, domin jam’iyya ba ta taɓa rasa matsala, saboda shugabannin da mambobinta duk mutane, kuma kowa yana da buƙatunsa.
Don haka dole a samu saɓani, a kuma samu son kai, ta yadda wani idan ba a yi masa yadda yake so ba, “to kai ba ka iya ba,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa.
A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa.
Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta a manyan teburan yanke shawara da ke tsara makomar al’ummarmu.”
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya zama dole ne bayan kiraye-kirayen da aka yi daga sassa daban-daban na mazabarsa, tare da yabawa irin sha’awar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, suka nuna wajen yin aiki tare da shi domin kawo “ci gaba mai tarihi da ban mamaki” a yankin.
Sanata Katung, yayin canza shekan tare da Hon. Daniel Amos da wasu abokansa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya nuna gamsuwa da “ayukan ci gaban” jam’iyyar APC a yankin Kaduna ta Kudu, yana mai cewa suna nuna adalci, daidaito, da ci gaba.
Ya ce, “Zamanin warewa da nuna bambanci, musamman a baya-bayan nan, yana gushewa, kuma ana maye gurbinsa da gwamnatin da ke da manufa da haɗin kai.”
“Saboda haka muna matsawa gaba domin tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun dore kuma sun yadu zuwa sauran al’ummomi da dama a yankin,” in ji shi.
Sanatan ya kuma roƙi abokai da abokan aiki da ba su goyi bayan wannan mataki nasa ba, da su mutunta ra’ayoyi daban-daban, tare da kaucewa barin siyasa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Ya ambaci kalmar Thomas Jefferson da cewa, “Ban taɓa ɗaukar bambanci a ra’ayi na siyasa, addini ko falsafa a matsayin dalilin janye ƙauna daga aboki ba.”
“A tare, mu ci gaba da zama ɗaya a manufa, mu dage da fata, kuma mu mai da hankali wajen samar da makoma mafi kyau ga al’ummar Mazabar Kaduna ta Kudu.”
Sanata Katung ya tabbatar da ƙudurinsa na ci gaba da aiki don haɗin kai da cigaba.
Daniel Karlmax