Leadership News Hausa:
2025-06-15@02:55:22 GMT

Jihohi 29 Sun Yi Watsi Da Ayyuka 270 Na Biliyoyin Naira

Published: 14th, February 2025 GMT

Jihohi 29 Sun Yi Watsi Da Ayyuka 270 Na Biliyoyin Naira

Binciken shiyya-shiyya na ayyukan ya nuna cewa shiyyar Kudu-maso-Kudu ta geo-siyasa ce ta kan gaba a jadawalin ayyuka 114 da aka yi watsi da su, inda Jihar Akwa Ibom ke kan gaba da ayyuka 87.

An nakalto cewa kawo yanzu gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya zuba Naira biliyan 47.93 cikin ayyuka 36 na kwamitin kudi da manufofin gwamnatin tarayya (FGPC) da ya gada, da kuma Naira biliyan 4.

04 cikin 51 na ayyukan gaggawa (EIPs) da ya gada daga gwamnatin da ta shude, adadin da ya kai Naira biliyan 51.96.

Shiyyar Arewa maso yamma ta biyo bayansu da ayyuka 44 da aka yi watsi da su, wanda jihar Zamfara kadai ke da ayyuka 33 da ba a kammala ba.

Yankin Kudu maso Gabas shi kuma yana biye da su da ayyuka 40, kuma Jihar Imo ce ta zo kan gaba da ayyuka 28 da ba a kammala ba. An ce gwamnatin Rochas Okorocha ta kaddamar da mafi yawan ayyukan, galibinsu asibitoci ne.

Yankin Kudu maso Yamma yana da ayyuka 34 da aka yi watsi da su, inda Jihar Ogun ke kan gaba da 23.

Shiyyar Arewa ta tsakiya itace ta hudu da ayyuka 33 inda Jihar Filato ke da 22 daga cikinsu. Ayyukan da ya gada na ababen more rayuwa na Naira biliyan 29, tsohon Gwamna Simon Lalong ne ya kaddamar da shi a wa’adinsa na biyu a kan karagar mulki, inda aka yi watsi da su saboda kararraki.

Yankin Arewa maso Gabas yana da mafi karancin ayyuka yayin da suke da 5 kacal da ba a kammala ba a kasar.

Jihohin Gombe da Taraba kowacce na da ayyuka guda biyu da suka gaza aiwatarwa,

Wani rahoto ya nuna cewa har yanzu gwamnatin Jihar Katsina ba ta kammala aikin noman injinan Windmill na Katsina da marigayi gwamna kuma shugaba Umaru Musa Yar’adua suka kaddamar a shekarar 2005 ba.

Gwamnatin tarayya ta karve aikin a 2007 kuma ta yi watsi da shi. Tun daga wancan lokaci aikin da aka tsara don samar da megawatts na wutar lantarki mai karfin megawatt 10, ya fuskanci tsaiko da yawa kuma har yanzu ba ya aiki duk da miliyoyin Naira da aka kashe a kai.

Har ila yau, shirin dam din Ingawa-Dallaje, shirin gwamnatin tarayya da ya kai Naira biliyan 4.3, da aka yi shi ne don samar da ruwa, da wuraren ban ruwa, da wutar lantarki ga al’ummomi da dama, an ba da fiye da rabin kudin kwangilar dan  kwangilar ya watsar da wurin sama da shekaru biyu da suka gabata.

A karamar Hukumar Kaita, aikin asibitin da ba a kammala ba tun daga gwamnatin Yar’adua har yanzu wurin na nan a kango.

Kazalika akwai wasu ayyuka da ba a kammala ba guda biyu su ne, ayyukan hanyar Katsina zuwa Kano. Aikin da ya taso daga Kano zuwa Gidan Mutum-Daya, shima an yi watsi da sauran kason da zai karasa Jihar Katsina saboda takaddamar biyan diyya ga mazauna yankin.

A Jihar Sokoto, babban dakin taro na asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Sokoto dake karamar Hukumar Wamakko da katafaren filin wasa na zamani mai dauke da dakin wasanni na cikin gida a unguwar Dange-Shuni, ayyuka ne guda biyu da gwamnatin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta karshe ta fara amma ba a kammala ba.

Duk da cewa an fara aikin gine-gine a harabar asibitin koyarwa da filin wasa a shekarar 2021 da 2022, kuma an kai matakin ci gaba kafin ficewar gwamnatin da ta gabata a halin yanzu an yi watsi da duka ayyukan biyu.

Wata majiyar gwamnati da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa, baya ga ayyukan da ba sa cikin jerin sunayen gwamnati mai ci a yanzu, akwai bukatar a sake duba sharudan kwangila don ganin ko matakin aikin da aka bayar ya yi daidai da biyan ‘yan kwangilar ko a a.

Wasu gungun mazauna yankin na Kasarawa da ke daura da ayyukan biyu sun yi kira ga gwamnati mai ci da ta farfado da su.

A Jihar Gombe wasu ayyuka guda biyu da tsohon Gwamna Ibrahim Dankwambo ya kaddamar an yi watsi da su a karkashin shugabancin Gwamna Inuwa Yahaya.

Ayyukan su ne, wurin shakatawa na Rainbow Amusement Park kusa da sanannen Rainbow Roundabout a babban birni da kuma da’irar zirga-zirga a Tashar Dukku, wadanda duka ba a kammala su ba sama da shekaru shida.

A Jihar Taraba ma, an yi watsi da wasu ayyuka da suka hada da titin Marabar Baisa-Kurmi da Marigayi Gwamna Danbaba Suntai ya kaddamar da kuma ayyukan ruwan Jalingo da Gwamna Darius Ishaku ya fara. Duk da an ba da umarni, gwamnatocin da suka biyo baya ba su kammala wadannan ayyukan ba. Gidan Lambun Ishaku na biliyoyin Naira shima ya kasance bai kammala ba.

Aikin titin Shafa Roundabout-Sango-Old Airport Road mai tsawon kilomita 2.8, wanda aka fara shekaru hudu da suka gabata, bai samu ci gaba kadan ba tun daga watan Janairun 2023, wanda ya bar mazauna cikin takaici.

Bugu da kari, aikin gina titinan Jihar Bayelsa Douye Diri na shekarar 2021, wanda aka bayar a kan Naira biliyan 4.8, ya tsaya cak bayan wani aikin magudanar ruwa.

A Zamfara, ayyukan da aka yi watsi da su sun hada da kiwon lafiya, samar da wutar lantarki, da inganta hanyoyi a kananan hukumomi 14, inda ba a kammala ayyukan samar da wutar lantarki a kananan hukumomi da dama ba. An yi watsi da asibitin Farida da muhimman ayyukan tituna irin su Gusau-Yelwa Samaru da Kucheri-Bilbis-Danjibga, lamarin da ya jawo koke-koke tsakanin al’umma.

Kebbi na da ayyuka guda hudu da aka yi watsi da su, wadanda suka hada da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da NYSC na dindindin a Dakingari, yayin da ayyukan da aka gada na kayayyakin more rayuwa na Naira biliyan 29 a Filato daga tsohon Gwamna Lalong suka tsaya cik saboda kararraki.

A Jihar Neja, har yanzu ba a kammala wasu muhimman hanyoyi irin su Minna-Sarikin Pawa-Kaduna da Katcha-Agaie-Baro, wadanda tsoffin shugabannin kasa Obasanjo da Jonathan suka kaddamar. Titin Mokwa-Bokani-Tegina-Birni Gera, wanda shi ma Jonathan ya kaddamar, ba a kammala shi ba.

Al’ummar Isanlu-Isin da ke yankin Kwara ta Kudu sun kuma bayyana damuwarsu kan yadda aka yi watsi da hanyar Oke Onigbin-Isanlu Isin mai tsawon kilomita 11.

LEADERSHIP Sunday ta ruwaito cewa gwamnatin Marigayi Gwamna Mohammed Lawal (1999-2003) ce ta bayar da wannan aikin amma ba a kammala aikin ba.

Wani shugaban al’ummar Isanlu-Isin, Cif Joshua Oloyede, ya roki gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak da ya ba da fifiko wajen kammala aikin.

Gwamnatoci da suka gaje su a Jihar Kogi ba su kammala ayyukan Otal din Kogi da na Confluence Beach ba.

Baya ga gwamnatin Alhaji Ibrahim Idris da ta yi yunkurin farfado da shi, tsarin ya lalace.

Haka kuma an bar Otal din Kogi da ke gidan gwamnati, Lokoja.

A Jihar Binuwai, ayyukan da aka yi watsi da su sun hada da tashar jirgin saman dakon kaya na Makurdi wanda kudinsa ya haura Naira biliyan 38, wanda tsohuwar gwamnatin gwamna Samuel Ortom ta gina; Kamfanin Tumatir da ke Wannnune a karamar Hukumar Tarka wanda gwamnatin George Akume ta fara; Kamfanin Sarrafa Doya, wanda gwamnatin Jibrilu ta fara; Titin Alaide Mabkine-Obarike-Ito mai tsawon kilomita 121 wanda gwamnatin da ta shude ta Ortom ta fara kuma ta yi watsi da shi.

Ayyukan da aka yi watsi da su a Jihar Osun sun hada da kamfanin Osogbo Steel Rolling Mill na gwamnatin tarayya da kuma kamfanin samar da kayan aikin Nigeria Machine Tools da ke Osogbo, yayin da kamfanin sarrafa Cocoa Ede da Five Star Hotel, Osogbo da kuma Osun State Pharmaceutical Company, Osogbo wanda mallakin gwamnatin Jihar ne.

Wani shugaban al’ummar Osogbo, Alhaji Rasak Remi Adejumobis, ya koka da yadda aka yi watsi da ayyukan da gangan, duk da dimbin jarin kudaden da aka kashe, ya kara da cewa kammala su zai sa al’umma su karu  wajen samun ayyukan yi da sauran ayyuka.

Yawancin ayyukan da aka yi watsi da su a Jihar Ondo, musamman hanyoyin da Marigayi Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya kaddamar, sun hada da aikin gyaran titin Ijoka, gadar sama da ke kasuwar Onyearugbulem, da titin hada-hada na Oda, da kuma hanyoyin cikin gida daban-daban a fadin jihar.

Haka kuma gwamnatocin da suka biyo baya sun bar madatsar ruwan Owena Multipurpose da ke Igbara Oke, wanda Marigayi Gwamna Olusegun Agagu ya fara, bai kammala ba. Wata majiyar gwamnati ta bayyana kalubalen tattalin a matsayin dalilin da ya aka samu tsaikon.

A Jihar Ogun, muhimman ayyukan da aka yi watsi da su sun hada da makarantar Polytechnic ta Ipokia, da makarantu 24 na model, da kuma cibiyar kasuwanci ta zamani a Abeokuta. Solomon Bankole, shugaban kungiyoyin fararen hula na jihar, ya bukaci Gwamna Dapo Abiodun ya kammala su.

Jihar Ekiti na da aiki a wuraren yawon bude ido na miliyoyin Naira da aka yi watsi da su, wanda Sanatoci uku suka gudanar a shekarar 2012. Aikin da aka yi a Ureje Water Works, Ado-Ekiti, bai kammala ba, sai manyan gine-gine biyu kacal ya rage bayan dan kwangilar ya gudu da kudaden.

Haka kuma Jihar Kuros Riba tana da ayyuka da dama da suka tsaya cak, wadanda suka hada da Piles and Pylons a unguwar Awi, tashar ruwa ta Bakassi Deep Sea Port, babban titi mai nisan kilomita 276, filin jirgin saman Cargo na Cally Airline a Obudu, da dai sauransu.

Aikin Monorail na Jihar Rivers a Fatakwal, wanda Gwamna Chibuike Rotimi Amaechi ya kaddamar a shekarar 2012, har yanzu bai kammala ba duk da Dala miliyan 400 da aka kashe a wurin. Hakazalika an yi watsi da makarantar Sapele Polytechnic ta Jihar Delta da gadar Ayakoromo, duk da cewa ana ci gaba da aikin gadar a cewar kwamishinan ayyuka na jihar.

A Jihar Ebonyi, ayyukan da aka yi watsi da su sun hada da cibiyar kasuwanci ta Jihar Ebonyi, otal mai lamba 5, otal din Rice City, kasuwar yankin Bishop Nnachi Okoro, da kuma wuraren noma a kananan hukumomin Izzi da Ikwo. Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamna Nwifuru da su kammala su.

Jihar Anambra na da ayyuka da dama da ba a kammala ba, kamar yankin Uku na Arms a Ishiagu da hanyar Ebenebe. Kwamishinan ayyuka na Jihar ya bayyana cewa an yi watsi da aikin Three Arms Zone ne domin aikin gidan gwamnati.

Gwamnatin da ta gabata a Jihar Imo kakashin Owelle Rochas Okorocha ta fara ayyuka da dama, irin su Imo Millennium Park da Asibiti, wadanda har yanzu ba a kammala su ba. Wasu asibitoci, duk da haka, an yi amfani da su ta hanyar hadin gwiwar masu zaman kansu da na jama’a.

Jihar Enugu kuma ta ga ayyukan da aka yi watsi da su, da suka hada da Cibiyar Dijital Bridge da Adada Dam, da nufin bunkasa noma. Aikin ruwan sama na Naira biliyan 30 na Gwamna Adam Oshiomhole a Birnin Benin, wanda magajinsa, Godwin Obaseki ya fara, bai kammala ba.

A Jihar Bayelsa, ayyuka na biliyoyin Naira kamar su masana’antar filastik ta Bayelsa, Bayelsa Palm, da Tower Hotel an yi watsi da su, kuma yanzu ciyawa ta mamaye su.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: gwamnati Niara ayyukan da aka yi watsi da su sun hada da da Marigayi Gwamna gwamnatin tarayya gwamnatin da ta an yi watsi da wutar lantarki Naira biliyan wanda Gwamna da gwamnatin har yanzu ba ga gwamnatin na da ayyuka ya kaddamar ga gwamnati

এছাড়াও পড়ুন:

Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa

A tsayin wadannan shekarun, Nijeriya ta fuskanci kalubale da dama da suka hada da fafutukar tabbatar da mulkin dimokuradiyya, siyasar yanki, rikita- rikitar addini da kabilanci da kuma gagarumar matsalar tsaro daga Kudu zuwa Arewa.

Mafi yawan al’ummar Nijeriya na bayyana shekaru 26 na mulkin dimokuradiyya a matsayin shekarun gurbataccen mulki, shekarun mulkin danniya da zalunci, cin hanci da rashawa, tabarbarewar tsaro, rugujewar tattalin arziki kana shekaru 26 na satar danyen mai, rashin wutar lantarki, koma baya a sha’anin ilimi, aikin gona da rashin ayyukan yi tare da hauhawar farashin mai da tsadar rayuwa.

Akasin murnar wannan ranar, kungiyoyi a Arewa da Kudu, jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula da na matasa da dalibai sun bayyana ‘yan siyasa a matsayin matsalar da ta dabaibaye kasar nan ba wai tsarin aikin gwamnati ba.

A mabambantan bayan su kungiyar dattawan Arewa ta ACF, kungiyar Yarbawa ta Afenifere da Ohanaeze ta Inyamurai sun bayyana amfani, nasarori, illa da matsalolin mulkin dimokuradiyya.

Kungiyar dattawan Arewa ta ce matukar ‘yan siyasa ba su watsar da tsattsauran ra’ayin su na rikau, talakawa ba za su mori romon mulkin dimokuradiyya ba. Ita kuwa kungiyar Yarbawa ta bayyana kima da tasirin mulkin dimokuradiyya ga kasa da ‘yan kasa, sai dai duk da kasawarsa a wasu bangarori ta ce shine tsari mafi inganci ga ‘yan Nijeriya.

Sai dai kungiyar Inyamurai ta bayyana cewar babu wata mafita ta samar da ci-gaba a Nijeriya illa canza fasalin kasa domin a baiwa kowane yanki damar bunkasa tattalin arzikin sa.

Haka ma kungiyoyi da dama sun koka ga gwamnati a kan ta gaggauta shawo kan matsalolin tsadar rayuwa, rage farashin mai da bunkasa tattalin arziki wadanda suka zama silar jefa al’umma a cikin kunci musamman a dalilin cire tallafin man fetur da wasu tsare-tsaren gwamnati masu tsauri.

A cewarsu maimakon shagalin buki, kamata ya yi a yi zaman jajantawa juna kan gurbatacciyar hanyar da shugabannin kasar mabambanta suka hau na rashin ci-gaba akasin ingantacciyar hanyar da shugabannin baya wadanda suka jagoranci samarwa kasar ‘yanci suka dora ta a kai.

Da yawan mutane sun yi tunanin daga shekarar 1999 zuwa yau matsalolin da ake fuskanta za su kau amma sai a ka ga akasin hakan. Abubuwan da ke ciwa jama’a tuwo a kwarya musamman sha’anin samar da hasken wutar lantarki har yanzu ba a shawo kan matsalar ba duk da irin makuddan kudaden da a ka narkar wadanda a ke ganin bai kamata a ce har yanzu babu tsayayyiyar wutar lantarki a Nijeriya.

A ra’ayin wasu gwamnatoci a mataki-mataki sun taka rawar gani. Idan da a ce babu mulkin dimokuradiyya da ba za a samu ‘yancin fadar albarkacin baki ba wanda shi kansa ci-gaba ne.

Haka ma a cewar su idan aka kalli kauyukan kasar nan a kananan hukumomi 774 zuwa yau an samu ci-gaba domin a can baya ba haka suke ba. Sai dai tabbas ci-gaban ba yadda a ka zata ba ne. Watakila gwamnatocin ba su samu kudade yadda ya kamata ba, wasu kuma na kukan matsalar daga hannun shugabanni take.

Mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a tsayin wadannan shekaru mulki ne da ke cike da rudu da kwamacalar siyasa daban-daban. A wanann rahoton za mu gabatar da muhimman abubuwan da dama da suka faru a kowace gwamnatin dimokuradiyya daga Obasanjo, ‘Yar’Adua, Jonathan, Buhari zuwa Tinubu da ke jan zaren mulki a yau.

 

Abubuwan Tunawa A Gwamnatin Obasanjo (1999-2007)

A jiya da yau a kan tuna da Gwamnatin Obasanjo a 1999-2007 ta hanyar kafa Hukumomin Yaki da Almundana da Kudaden Al’umma (EFCC) da (ICPC) tare da karfafawa Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata domin yaki da cin hanci da rashawa. Gurbatattun ‘yan siyasa da mutane da dama sun shiga hannu tare da gurfana a kotu zuwa daurewa a kurkuku a wancan lokacin.

Wasu daga cikin nasarorin da za a iya cewa gwamnatin Obasanjo ta samarwa al’ummarta akwai rattaba hannun shigowa da kamfunan sadarwa wanda ya zama silar samar da wayoyin hannu na GSM wanda daga lokacin zuwa yau kusan babu wani gida a Nijeriya da ba a mallakin wayar tafi-da-gidanka ba.

Gwamnatin Obasanjo wadda aka samu tabarbarewar tsaro da rikita- riikitar kabilanci a mulkinsa haka ma a mulkin sa an shaidi yawaitar faduwar jiragen sama ciki har da jirgin ADC wanda ya dauki rayuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido da muhimman mutane a 2006.

Gwamnatin Obasanjo ta yi matukar kokarin samarwa Nijeriya afuwar bashin zunzurutun kudi har dala Biliyan 18 daga Paris da London wanda ya jima yana ciwa kasar nan tuwo a kwarya.

Bugu da kari a zamanin mulkin Obasanjo ne siyasar ko- a- mutu- ko- a- yi-rai ta samu gindin zama ta yadda aka rika sarawa ko babu gaba ga duk wani ko wadanda suka yi kokarin shiga gona ko huruminsa. Obasanjo a 2007 a kokarin sharewa marigayi ‘Yar’Adua hanyar zama shugaban kasa, ya jagoranci gudanar da kazamin zabe mafi muni a Nijeriya wanda ke cike da aika-aika da murdiyar zabe.

Haka ma Obasanjo ya so yi wa mulkin dimokuradiyya fyade a yayin neman zarcewa saman mulki a wa’adi na uku lamarin da ‘yan Nijeriya suka sa kafa suka shure tare da Allah-wadai kan kokarin yin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasa, abin da ya kawo karshen bukatarsa wadda hakarsa ta kasa cimma ruwa.

 

Umaru ‘Yar’Adua (2007-2010)

Umaru Musa ‘Yar’Adua shine shugaban Nijeriya daga Mayu 2007 zuwa 5 ga Mayu 2010 a lokacin da ya yi bankwana da duniya yana a saman mulki.

‘Yar’Adua ne shugaban kasa na farko a tarihi da ya fara bayyana kadarorin da ya mallaka a bayyane tun kafin ya shiga ofis. Haka ma a fili ya fito ya bayyanawa duniya cewar zaben da ya kawo shi saman mulki cike yake da ta’addanci, murdiya da sabawa dokokin zabe.

Haka ma gwamnatin Matawallen na Katsina ta taka rawar gani wajen rage farashin man fetur daga farashin da yake akai zuwa naira 65 a kowace lita. Dukkanin gwamnatocin baya kara farashin mai suke yi, ita kuwa ta ‘Yar’Adua saukar da farashin ta yi. Kazalika takaitacciyar gwamnatin ‘Yar’Adua wadda ba ta yi tsawon rai ba ta cancanci a yaba mata wajen kawo gyara ga dokokin zabe.

Baya ga wannan a mulkinsa ba za a manta da yadda ya sa kafa ya sabawa tsarin mulki wajen rashin hannuntawa mataimakinsa Jonathan ragamar mulki ba a yayin da ya bar kasa zuwa duba lafiyarsa a Saudi Arabiya. Sai dai ‘yan Nijeriya masu kishi da hangen nesa sun tashi tsaye suka jagoranci gyara babbar matsalar tare da tabbatar da zaman Jonathan a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Haka ma gwamnatin ‘Yar’Adua ta samu nasarar kawo karshen ta’addancin tsagerun yankin Neja-Delta da ke talauta kasa ta hanyar yi masu afuwa suka ajiye mukamai tare da tallafa masu a shirin musamman wanda a lokacin ya kawo karshen ta’addanci a yankin mai albarkar man fetur.

 

Goodluck Jonathan (2010-2015)

A zamanin gwamnatin Jonathan ‘yan ta’addan Boko-Haram sun ci karensu ba babbaka ta yadda al’ummar kasa suka rika bacci da ido daya a gwamnatin Jonathan wanda shine shugaban kasa na farko da ya fito daga yankin Kudu-Maso-Kudu.

Sace ‘yan matan Chibok 100 da mayakan Boko-Haram suka yi awon gaba da su a makarantar mata a Jihar Borno a Afrilu 2014 lamari ne da ya yi matukar jan hankalin al’ummar ciki da wajen kasar nan.

Jonathan ya zama shugaban kasa na farko a tarihi kasar nan da ya sha kasa a zabe yana kan gadon mulki. Fitowa fili da ya yi ya karbi faduwa zabe tare da taya Muhammadu Buhari murna ya daga darajarsa da samar masa kima da dattako tare da tabbatar da karfin mulkin dimokuradiyya.

 

Muhammadu Buhari (2015- 2023)

Muhammadu Buhari wanda ya zama shugaban kasa a 2015 bayan ya sha kaye a zabukan 2003, 2007 da 2011, ya sake lashe zaben 2019 da gagarumar nasara.

Gwamnatin Buhari wadda ta yi kaurin suna wajen yekuwar yaki da cin hanci da rashawa, ta fadi kasa warwas ta hanyar kasa magance yawaitar cin hanci a fannoni da dama lamarin da jama’a ke ganin batun yaki da cin hanci suna ne kawai a gwamnatin Buhari domin kuwa a yayin da ake gurfanar da magoya bayan PDP a kotu, takwarorinsu na APC suna ci-gaba da cin karensu ba babbbaka a matsayin shafaffu da mai.

Bugu da kari gwamnatin Buhari ta kasance ta farko a dimokuradiyyar kasar nan da ta rika kawar da kai ga mutunta kundin tsarin mulkin kasa ta hanyar katsalandan ga sashen shari’a da rashin mutunta umurnin kotuna.

Misali kotuna daya bayan daya har guda tara sun bayar da belin Sambo Dasuki rsohon mashawarci na musamman kan sha’anin tsaro a gwamnatin Jonathan amma kuma gwamnatin Buhari ta kasa sakinsa a daurin da ta yi masa a kusan shekaru hudu kan badakalar kudin makamai.

A karkashin mulkin dimokuradiyya a zamanin Buhari al’ummar Nijeriya sun fuskanci yawaitar kisan gilla, garkuwa da mutane da ta’addancin Fulani fiye da kowane lokaci gabaninsa wanda bakidaya al’umma musamman a yankin Arewa suke cikin zullumi da fargaba. Haka ma Buhari zai ci-gaba da zama a cikin tarihi a matsayin shugaban kasa da ya kwashe kwanaki 217 wajen duba lafiyarsa a wajen kasar nan.

 

Bola Tinubu 2023-

A shekaru biyu na mulkin Bola Ahmad Tinubu al’ummar kasa na kuka da kokawa da tsare- tsare da manufofin gwamnatinsa masu tsauri ta yadda da yawa ke kewa da kwadayin mulkin PDP wanda rayuwa ke da sauki a mulkin ta.

Cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi a jawabinsa na karbar mulki a 2023 shine babban abin da ya dauki hankalin jama’a tare da girgiza su musamman bisa ga radadi da kuncin da matakin ya jefa kasa da ‘yan kasa a ciki wanda ya haddasa tsada da karancin man fetur a lokaci daya.

Ya zuwa yanzu al’umma na cike da kunci a dalilin hauhawar farashin dukkanin abubuwan da rai ke bukata ta yadda abubuwa da dama musamman abinci ke gagarar talaka.

Duk da cewar farashin abinci yana tashi sama a fadin kasa a tsayin shekaru, amma yanayin a wannan lokacin ya ta’azzara ne sosai a bisa ga illar shiraruwan gwamnati musamman cire tallafin man fetur, faduwar darajar naira da sauransu.

 

Karuwar Talauci

Al’ummar Nijeriya da ke fama da talauci a zamanin gwamnafin da ta gabata sun kara talaucewa sosai a cikin shekaru biyu na mulkin Tinubu ta yadda a yau suke zumudin zuwan lokacin zabe.

Tsananin talaucin da al’umma ke fama da shi a yanzu, ya sa mafi yawan jama’a kasancewa cikin kuka da kokawa da yadda mulkin Tinubu ya zo masu wanda a baya suke fatar samun saukin al’amurra bayan karewar gwamnatin da ta gabata, amma sai gashi talaucin da ake fama da shi a yanzu ya fi na baya tsanani.

 

Matsalolin Tsaro

Duk da matakan da gwamnati ke dauka na kokarin samar da ingantaccen tsaro har zuwa yanzu ‘yan ta’adda na ci-gaba da cin karensu ba babbaka ta yadda suke hanawa al’umma bacci da idanu biyu wanda kasawa ce karara ga gwamnati a shekaru 26 na mulkin dimokuradiyya amma a kullum tsaron kasa kara tabarbarewa yake yi.

A yayin jin ra’ayin mabanbantan al’ummar kasa daga Arewa har Kudu kan amfani da alfanun da suka amfana da shi na romon mulkin dimokuradiyya, da yawa daga ciki sun bayyana shekaru 26 na dimokuradiyya a Nijeriya a matsayin shekarun gurbatacciyar dimokuradiyya, mulkin fatara da talauci, mulkin rikice-rikice da tashe-tashen hankula.

Bugu da kari jama’a sun fassara 26 a matsayin shekarun cin hanci da rashawa, shekarun sata da wawashe kudaden al’umma, kazalika shekarun karawa masu karfi karfi da kuma ci- da gumin talaka.

A kan wannan karara a yayin da wasu ke bayyana mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a matsayin wata hular baka ce wasu kuwa cewa suke yi Shekaru 26 Na Mulkin Dimokuradiyya A Nijeriya: Da Dadi, Ba Badi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa
  • Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa
  • Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025
  • Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa
  • Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6
  • NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
  • ICPC Ta Gurfanar Da Ma’aikacin Kotu Bisa Badakalar Naira Miliyan 9.2
  • An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe
  • Zan Ci Gaba Da Ɓata Wa Masu Sukar Tinubu Rai Da Ayyuka – Wike
  • Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai