A yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da shugaban gwamnatin kasar Jamus Friedrich Merz, bisa gayyatarsa da aka yi.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da Jamus suna raya dangantakar dake tsakaninsu bisa girmama juna, da amincewa da bambance-bambance, da hadin gwiwa don samun moriyar juna, kuma akwai bukatar bangarorin biyu su yi kokari tare don tabbatar da raya dangantakarsu yadda ya kamata.

Ya ce, da farko dai, ya kamata a yi imani da juna a fannin siyasa tsakanin kasashen biyu. Na biyu kuma, ya kamata a kara inganta dangantakarsu, wato ci gaba da hadin gwiwa a fannonin da suka riga sun hada hannu kamar su kera motoci, da injuna, da kuma masana’antar sinadarai da kuma kara fadada hadin gwiwarsu a sabbin fannoni kamar fasahar AI, da fasahar quantum da sauransu. Na uku kuma, ya kamata a kara karfi wajen hadin gwiwarsu, watau Sin tana fatan kasar Jamus za ta kara samar da goyon baya da sauki da gabatar da manufofi don inganta zuba jari da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a samar da yanayin cinikayya mai adalci da daidaito da gudanar da komai a bude, ga kamfanonin kasar Sin.

A nasa bangare, Merz ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin kasar Jamus za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da kokarin raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu bisa halin da ake ciki yadda ya kamata. Har ila yau, ya ce kasar Jamus tana begen kara mu’amala da hadin gwiwa da kasar Sin, da bude kofarta ga kasashen waje da samun moriyar juna, da sa kaimi ga yin ciniki cikin adalci, da tabbatar da zaman lafiya a duniya, da kuma tinkarar kalubalen duniya kamar sauyin yanayi tare. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Jamus

এছাড়াও পড়ুন:

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka 
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar