Majiyoyin watsa labaran Iran sun musanta da’awar cewa: Amurka ta bukaci ziyarar cibiyoyin sojojin Iran

Wasu majiyoyi masu tushe sun musanta ingancin da’awar jita-jita na baya-bayan nan game da bukatar Amurka ta neman ziyartar cibiyoyin sojojin Iran, tare da bayyana su a matsayin maganganu marasa tushe.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim, rahoton da ya shafi bukatar Amurka na ziyartar wuraren soji, cibiyar makamashin nukiliya da kuma wuraren bincike na Iran cikin makonni masu zuwa, labarai ne marasa tushe ballantana makama.

Haka zalika majiyoyin sun musanta ikirarin da ake dangantawa da ministan harkokin wajen Iraki na cewa “ya yi kira ga Iran da ta fice daga Iraki,” suna masu jaddada cewa ba a taba yin irin wadannan kalamai ba.

Tun da farko dai rahotanni sun da’awar cewa: Amurka ta bukaci Iran da ta bata damar kai ziyara tare da duba wuraren bincike na sojojin Iran guda 31, da cibiyoyin makamashin nukiliya a cikin makonni masu zuwa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

‘Aikin Yan Uba Ne’ — Yahaya Bello Ya Karyata Zargin Sha’awar Takarar Shugaban Kasa A 2027

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kara Haske kan Batun Inganta Sinadarin Uranium Da Zamanta Da Amurka
  • ‘Aikin Yan Uba Ne’ — Yahaya Bello Ya Karyata Zargin Sha’awar Takarar Shugaban Kasa A 2027
  • Limamin Masallacin Jumma’a A Nan Tehran Ya Yi Magana Dangane Da Kwatar Garin Khurramshar Daga Sojojin Sadam
  • Allah Ya Isa: Shugaban PDP Damagun ya musanta zargin yi wa APC aiki
  •  Nahiyar Afirka Ta Kafa Cibiyar Tattara Bayanai Akan Yanayi
  • Sojojin Yemen Sun Kai Wa Filin Jirgin Saman “Ben Gorion” Hari Sau Biyu A Yau Alhamis
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Ce; Ba Ta Gaggawar Neman Kulla Alaka Da Kasar Siriya
  • Gwamnatin Afirka Ta Kudu Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Turawa ‘Yan Kasar Fararen Fata
  • Za’a Gudanar Da Tattaunawa Zagaye Na 5 Tsakanin Amurka Da Iran A Ranar 23-Afrilu A Roma