Leadership News Hausa:
2025-11-03@03:09:25 GMT

Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

Published: 24th, May 2025 GMT

Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

PDP na fama da rikicin cikin gida mafi muni a tarihin jam’iyyar. Tun lokacin da jam’iyyar ta rasa shugabanci a 2015, ta ci gaba da fuskantar matsaloli wajen magance rikicin da take fama da shi. Ko wani zabe yana zuwa da nashi kalubalan, yana bayyana cin amana na cikin jam’iyya.

Zaben 2023, jam’iyyar ta bai wa Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, wanda shi dan Arewa ne, inda lamarin ya haifar da fushi na masu ruwa da tsaki daga kudancin kasar nan, musamman daga wajen ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike.

Haka ma a daidai lokacin da ake kara fuskantar zaben 2027, wannan yanayi na sake kara bayyana adaidai lokacin da Atiku ke kokarin samun tikitin jam’iyyar. A lokaci guda, Wike ya bayyana matsayinsa a fili kan zaben da ke tafe.

A wani taron manema labarai na kwanan nan, tsohon gwamnan Jihar Ribas ya yi gargadin kar jam’iyyar ta bai wa wani dan takarar shugaban kasa daga yankin Arewa, ya yi hasashen cewa PDP za ta sake shan kaye idan har ta kara yin wannan kuskuren.

Ko shugabannin PDP sun ji dadin hakan ko ba su ji dadin ba, matsayin Wike ya dace da mutanen Kudu, wadanda ke ganin yankinsu ya cancanta ya kammala shugabancin shekaru takwas kafin mulki ya dawo Arewacin Nijeriya.

Matsalar tsarin karba-karba ta kunno kai ne bayan da Atiku ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, madadin kira na neman dan takara daga Kudu.

Wannan ya bai wa Wike damar yakar PDP. Lmarin da ya kulla dangantaka da APC, wanda ya sanya shi ya zama babban abokin hamayya a jam’iyyar.

Yanzu, PDP na fuskantar wannan yanayin na bin tsarin karba-karba kafin 2027. Masu nazarin harkokin siyasa na jiran ganin yadda za ta kaya a wannan lamari tsakanin Kudu da Arewa.

Duk da haka, yayin da masu ruwa da tsaki daga Arewa ke ganin cewa yawansu na iya taimaka wa PDP dawo da iko, abokansu daga Kudu sun yi imani da cewa fitar da dan takarar shugaban kasa daga yankinsu zai taimaka wa jam’iyyar wajen dawo da wurare masu mahimmanci da suka rasa.

Dangane da wannan, Saraki na jagorantar kwamitin sulhu da ke fuskantar kalubale masu yawan gaske. An da dora masa alhakkin dawo da martaban jam’iyyar da sulhunta tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar masu mukami da wadanda ba su da mukami.

An dai nada Saraki wannan matsayin ne saboda dabarunsa na tsare-tsare da iya yin sulhu, ya shawo kan manyan batutuwan siyasa a cikin tarihinsa. Haka ma ko a lokacin da ya zama shugaban majalisar dattawa ya samu nasarar hada kan ‘yan majalisa a cikin yanayi na muni wajen shugabanci.

Duk abin da Saraki ke shirin yi, matakan sulhunsa dole ne su hada da shirye-shiryen da za su gamsar da masu goyon bayan Wike, sake hada masu ruwa da tsaki daga kowane yanki da kuma sake fasalta rabon mukamai na jam’iyyar don kawo daidaiton siyasa a Nijeriya. Wannan aiki ne mai wahala, amma ‘yan Nijeriya da dama na ganin cewa Saraki yana da kwarewar siyasa da zai iya yin wannan jan aikin idan har jam’iyyar ta ba shi dama.

Idan har kokarin sulhu na Saraki ya gaza, to a bayyana yake PDP za ta rasa madafa, sannan za ta kara fadawa cikin Rashin tabbas. Amma idan ya yi nasara, zai iya dawo da martabar siyasar jam’iyyar a Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Saraki takarar shugaban kasa jam iyyar ta a jam iyyar

এছাড়াও পড়ুন:

Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka

A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya.

Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar.

Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 

“Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar da ‘yan ta’addan Musulmai da ke aikata wannan ta’asar,” in ji Hegseth.

Trump dai ya yi wannan barazanar ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, inda ya ce Amurka za ta dakatar da duk tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma tana iya “shiga ƙasar da ƙarfin soji domin share ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci.”

“Idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wata tallafi, kuma mai yiwuwa ta shiga wannan ƙasar, ta cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’addan Musulmai masu zafin kishin addini,” in ji Trump.

Ya kuma gargaɗi gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta ɗaukar mataki, yana cewa idan Amurka ta kai farmaki “za ta yi shi cikin sauri, da tsananin ƙarfi, da gamsuwa.”

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan Trump ya mayar da Nijeriya cikin jerin ƙasashen da za a sanyawa ido, yana zargin cewa “ana yi wa Kiristoci kisan gilla” a hannun ƙungiyoyin Musulmi masu tsattsauran ra’ayi.

Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.

“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.

A cewar mai ba wa Tinubun shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, za a yi ganawa tsakanin Shugaba Tinubu da Shugaba Trump “a cikin kwanaki kaɗan masu zuwa” domin tattaunawa da warware wannan saɓanin fahimta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku