Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai
Published: 23rd, May 2025 GMT
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar, Mr. Xi Jinping, a kwanakin baya ya yi muhimmin bayani game da aikin raya harkoki masu nasaba da wayewar kai a kasarsa, inda ya ce, ci gaban dukkanin fannonin samar da ababen more rayuwa da kuma wayewar kai, muhimmiyar alama ce ta zamantarwa mai salon kasar Sin.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa hadin kan jama’a bisa tunanin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin na sabon zamani, da mai da hankali kan wayar da kan al’umma, da sa kaimin raya al’adu da kuma da’a a tsakanin al’umma, sa’an nan kuma a karfafa ayyukan ba da jagoranci, da zurfafa yin gyare-gyare da kirkire-kirkire, da sa kowa ya shiga wannan harka, domin samar da karin kuzari wajen gina kasa mai karfi da farfado da al’ummar kasar.
A yau Juma’a ne aka bude taron karrama wadanda suka ba da muhimmiyar gudummawa wajen raya wayewar kan al’umma a kasar Sin, inda kuma aka sanar da wannan muhimmin bayanin da shugaba Xi ya yi. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Nuna Damuwa Akan Tabarbarewar Yanayin “Yan Hijira A Gabashin Kasar Chadi
MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su.
Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida.
Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39.
Sanarwar ta MDD ta ci gaba da cewa; Wannan sabon adadin ya karu ne akan wasu ‘yan hijirar miliyan daya da sun dade da shiga gabashin Chadi, tun daga fara yakin basasar Sudan a a tsakiyar watan Aprilu na 2023.
Mai Magana da yawun MDD Stephen Dujarric ya ce; siyasar da kasar Chadi take aiki da ita bude kofofinta ga ‘yan hijirar ne ya bayar da wannan damar.
Haka nan kuma ya bayyana cewa wuraren da aka ware domin tarbar ‘yan hijirar a gabashin Sudan din sun yi kadan’ sannan ya kara da cewa; mafi yawancin masu kwararowar mata ne da kananan yara da su ka kadu saboda yakin da ake yi a can Sudan.