Kungiyar Ta’addanci Ta ISIS Ta Zargi Shugaban Gwamnatin Siriya Da Kauce Hanya Madaidaiciya
Published: 23rd, May 2025 GMT
Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta zargi shugaban gwamantin kasar Siriya al-Julani da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai
Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta bayyana shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani a matsayin azzalumi wanda ya sayar da addininsa tare da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai.
A cikin wani sako na addini, a kokarinta na jan hankali masu saurarenta wadanda ta kira su “masu hijira saboda Allah,” kungiyar ta’addanci ta ISIS ta fitar da wani kira na farfaganda ga wasu ‘yan kasashen waje da kuma sabbin hukumomin tsaro na gwamnatin Siriya, kungiyar ISIS ta yi kira ga ‘yan kasashen waje da ke kasar Siriya da su tuba su daina yi wa sabon shugaban gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani biyayya da hidima, wanda ta bayyana shi a matsayin azzalumin da ya sayar da addininsa tare da yin sujada a kofar mashigar kafirai.
Sakon kungiyar ta ISIS na kunshe da gargadi mai tsanani ga wadanda ke ci gaba da aiki a cikin sabuwar gwamnatin Siriya. Har ila yau, sakon ya hada da barazanar kai hare-haren soji, da nuna kasancewar mambobinta da ta tura su zuwa yankunan karkara, tare da yin barazanar mayar da martani ga duk wani mataki da aka dauka kanta.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: gwamnatin Siriya
এছাড়াও পড়ুন:
Yakin Gaza : Tarayyar Turai za ta sake nazari kan Yarjejeniyarta da Isra’ila
Bayan sabon farmakin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, kasashen Yamma na kokarin kara matsin lamba kan Isra’ila, wacce ta kauda kai kan kiraye kirayen da duniya ke yi na ta dakatar da yakin a Gaza.
Kungiyar ta EU, ta kara mastin lamba ta hanyar sake nazari kan yarjejeniyarta da Isra’ila ta tsawon shekaru 25 dake a tsakaninsu.
Tunda farko dama kasashen kasashen Canada-Faransa da Ingila sun sanar da yin Allah wadai da farmakin kasa na soja na sojojin Isra’ila a Gaza.
Baya ga hakan kuma Birtaniyya a ranar Talata ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci da Isra’ila.
Ita ma kiasar Sweden, ta yi kira da a kakaba takunkumi ga membobin gwamnatin Isra’ila.
Bayanai sun ce yanzu haka matakan da wasu kasashen yamma ke doka , ya hadassa sabani tsakanin kasashe 27 na Tarayyar Turai.