Kotu ta bai wa EFCC izinin binciken sayar da filin musabaƙar Alƙur’ani na N3.5bn a Kano
Published: 23rd, May 2025 GMT
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S.M. Shuaibu ta ƙi amincewa da buƙatar wasu mambobin Kwamitin Musabaƙar Alƙur’ani da ke son a hana EFCC bincike kan yadda aka sayar da wani fili mai darajar Naira biliyan 3.5.
Filin da ake magana a kai yana bayan titin Ahmadu Bello Way, kuma yana da faɗin hekta biyu.
Tsohon Gwamnan Sojan Kano, Kanal Abdullahi Wase ne, ya bayar da filin don a gina katafaren waje da za a riƙa gudanar da musabaƙar Alƙur’ani duk shekara.
Amma daga baya sai wasu mambobin kwamitin suka ga an gina gidaje 38 a filin ba tare da sanin su ba.
Hakan ne ya sa a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, wasu daga cikin amintattun kwamitin suka kai wa EFCC ƙara, domin ta binciki yadda aka sayar da filin a ɓoye.
Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Sheikh Ibrahim Shehu Mai Hula, Sheikh Gwani Yahuza Danzarga, Tijjani Bala Kalarawi, Aliyu Harazimi, Barrister Saidu Koki, Ado Shehu Maibargo, Dokta Aliyu Darma, Tijjani Mai Lafiya Sanka, Alhaji Tukur Gadanya da Alhaji Sabiu Bako.
Sun buƙaci kotu ta hana EFCC gayyatarsu ko cafke su dangane da wannan batu, sun dogar da wasu sashe na kundin tsarin mulki da yarjejeniyar kare haƙƙin ɗan adam ta Afirka.
Amma kotu ta ce EFCC na da hurumin gudanar da bincike kamar yadda doka ta tanadar, kuma babu kotun da za ta hana hakan, musamman idan ana zargin aikata laifi.
Don haka, kotu ta bayyana cewa waɗana ake ƙara su biya Naira 250,000 ga waɗanda suka yi ƙararsu, saboda ɓata musu lokaci.
Lauyoyin da suka kare wanda ake ƙara – Sadiq Yahya da John Chukwu Eze – sun yaba da hukuncin kotun, yayin da lauyan masu ƙara, Yahaya Isa Abdulrasheed, ya ce za su ɗaukaka ƙara.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano
Al’ummar yankin Bachirawa a Jihar Kano sun yi ta maza sun cafke wasu matasa biyu da ake zargi da ƙwace waya a unguwar a yayin da ɓata-garin suke tsaka da ƙwacen.
Matasan dai sun tare wata mata ce a unguwar suka ƙwace mata waya, wanda hakan ya sa mutanen yankin suka yi kansu tare da kama su.
An samu nasarar karɓe wayar da suka amsa tare da ƙwace makaman da aka samu a hannunsu.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da haka bayan al’ummar sun miƙa waɗannan matasa ofishin ’yan sanda a ranar Juma’a.