Yan Majalisar Tarayya Na Katsina Sun Mara Wa Gwamna Dikko Radda Baya Don Takarar Zango Na Biyu
Published: 23rd, May 2025 GMT
Daga Bello Wakili
Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa.
An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa.
Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare.
‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna Radda, inda suka bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa da kuma wanda ke tafiyar da mulki cikin hadin kai.
Sun jaddada cewa gwamnatinsa ta samu gagarumin ci gaba wajen yaki da rashin tsaro, sauya fasalin ilimi, bunkasa noma, karfafa tattalin arziki da kuma karfafa al’umma.
A cewarsu, wadannan kokari sun sanya Jihar Katsina ta fara tafiya kan turbar ci gaba mai dorewa da walwala.
Don karfafa wannan matsaya, Sanata Abdulaziz Yar’adua mai wakiltar mazabar Katsina ta Tsakiya, ya goyi bayan kudirin a madadin sauran sanatoci biyu daga jihar.
Ya ce su ma sanatocin sun amince da matsayar da ‘yan majalisar wakilai suka dauka, tare da bayyana Gwamna Radda a matsayin dan takarar gwamna daya tilo na jam’iyyar APC a zaben 2027.
‘Yan majalisar sun yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya da aminci ga yunkurin gwamnan na sake tsayawa takara, tare da kira ga dukkan ’ya’yan jihar Katsina da su hade kai domin ci gaba da tafiya a hanya daya ta dorewar cigaba da hadin kai.
Wannan hadin kai daga bangarorin majalisar wakilai da ta dattijai na nuna karuwar karfin siyasa ga Gwamna Radda yayin da zaben 2027 ke karatowa.
COV/BELLO WAKILI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yan majalisa Goyon Baya Mara Baya Takarar yan majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar: An Kashe Sojoji 10 A Wasu Hare-hare Biyu Na ‘Yan Ta’adda
Raundunar sojan jamhuriyar Nijar sun sanar da cewa, an kashe sojoji 10 da kuma jikkata wasu 15 a wasu hare-hare biyu da masu dauke da makamai su ka kai a yankin Telaberi da kudu masu yammacin kasar.
Yankin Telaberi dai yana cikin yankunan da masu dauke da makamai su ka fara kai hare-hare saboda kusancinta da iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso.
Bayanin na sojojin kasar ta Jamhuriyar Nijar wanda kafafen watsa labarun kasar su ka watsa ya kunshi cewa; Daruruwan masu dauke da bindiga sun kai hare-hare a kan sansanonin soja biyu da suke a yankin Telaberi da hakan ya yi sanadiyyar kashe sojoji 10 da kuma jikkatar wasu 15.”
Sai dai kuma sanarwar ta ce, sojojin sun yi nasarar kashe 41 daga cikin maharan.
A watan da ya shude ma dai kasar ta Nijar ta fuskanci hare-hare masu muni. Daga ciki da akwai wani kwanton bauna da aka yi wa sojoji da garin Agadas wanda ya ci rayukan 11 daga cikinsu. Haka nan kuma an kashe fararen hula 40 a wasu jerin hare-hare a fadin kasar a shekarar da ta gabata a kusa iya da Burkina Faso.
Tun daga 2015 ne dai sojojin kasar ta Nijar suke fuskantar hare-haren ta’addanci a cikin yankuna mabanbanta, musamman a yankunan da suke kan iyaka.
Yankin tafikin Chadi dai daya daga yankuann da suke da iyaka da Najeriya, Kamaru da Chadi, wanda yake da maboyar ‘yan kungiyoyin Bokoharam da kuam ISIS.
Kasashe uku da yammacin Afirka da su ka kafa tsarin Kwanfaderaliyya da su ne; Mali, Nijar da Burkina Faso, suna Shirin kafa rundunar soja ta hadaka mai mayaka 5000 domin fuskantar ‘yan ta’adda da tsararrun laifuka. Sanarwar hakan dai ta fito ne daga bakin ministan tsaron Nijar Salihu Mudi.