‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Na’urorin Zamani Daidai Lokacin Da Sojoji Ke Da Karancin Makamai -Zulum
Published: 23rd, May 2025 GMT
“’Yan kwanakin da suka gabata, na yi wata ganawa da Babban Hafsan Sojin Kasa, inda ya bay-yana min cewa; yana neman akalla jirage marasa matuka kimanin 32, domin kawo karshen wannan ta’addanci, wanda kuma abin da ya fada din gaskiya ne.
“Kowane jirgi maras matuki, na kai wa kimanin dala miliyan 5.5, don haka, me yasa ba za mu iya hada karfi da karfe wuri guda mu sayi jiragen ba, don bai wa harkar tsaro fifiko?
Har wa yau, ya bayyana kwarin gwiwar cewa; tare da bin tsarin da ya dace da hadin kai a tsa-kanin dukkanin bangarorin gwamnati, za a iya magance wadannan tashin hankula cikin gagga-wa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Boko Haram: Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kafa Sansanin Sojoji A Hong Ta Jihar Adamawa
Majalisar ta kuma umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da ta samar da kayayyakin agaji ga al’ummomin da hare-haren ya shafa domin bayar da agajin jin-kai.
Da yake gabatar da kudirin, Sanata Abbas, ya ce hare-haren da aka kai sun raba dubban mazauna karamar hukumar ta Hong da gidajensu, tare da lalata musu rayuwa.
Ya yi nuni da cewa, sake bullar ‘yan ta’addan ya zarce Adamawa hat zuwa jihohin Borno da Yobe, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp