Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza.

Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da  kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba.

Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya wacce ta dauki labarin tare da ambato wasu fitattun malaman na yahudawa da su ka rattaba hannu akan takardar, daga cikinsu har da Sharon Bruss, Roly Matalon, da Alisa Waiser, sai kuma wasu fitattun yahudawa a Amurkan.

Cody Edgerly wanda daya ne daga cikin wadanda su ka rattaba hannu akan takardar, kuma shugaban kiran, ya nuna abinda shugaban na kasar Amurka yake son yi da cewa tsallake iyaka ne wacce a baya ake tsammancin cewa ba za a taba ketare ta ba, amma ga shi tana faruwa a karkashin kawancen Trump da Netanyahu.

Haka nan kuma wasikar ta fadawa Falasdinawa cewa: Sakonmu a gare ku shi ne cewa, ba ku kadai ba ne,muna a tare da ku, kuma  kowane daya daga cikinsu a shirye yake ya yi yaki har kar karshen rayuwasa.

Rabbi Toba Spitzer ya bayyana abinda Trump din yake son aikatawa da cewa; “Babban zunubi ne.” Ya kuma yi tuni da abinda aka yi wa Falasdinawa a 1948 da  kungiyoyin Sahayoniya masu dauke da makamai su ka kori dubun dubatar Falasdinawa daga gidajensu.

Shi kuwa Rabbi Yusuf  Berman, cewa ya yi: Da alama Trump yana daukar kansa a matsayin mamallakin wannan duniya da yake da hakkin shimfida ikonsa a ko’ina a duniya.”

Haka nan kuma ya ce; koyarwar Attaura a fili take cewa; Trump mutum ne, ba shi ne mamallaki duniya ba, don haka ba shi da hakkin da zai raba Flasdinawa da kasarsu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa.

Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa.

Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba.

NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa

Wannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  • Saudiya Ta Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza A Gaban Kutun ICJ
  •  Manyan Malaman Roman Katolika Sun Fara Taron Zabar Paparoma
  •  Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
  • DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • HKI Tana Amfani Yunwa A Matsayin Makamin Yaki  A Kan Falasdinawa A Gaza
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Komawa Kan Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba
  • Lebanon:  Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut