Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi
Published: 12th, March 2025 GMT
Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci zafin rana mai tsanani a kwanaki masu zuwa, a wasu yankuna na Najeriya.
A cewar NiMet, jihohin da za su fi fuskantar wannan yanayi sun haɗa da Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nasarawa, Benuwai, Enugu, Anambra, Abiya, Ebonyi, Kuros Riba da Babban Birnin Tarayya.
Sauran yankunan da ake tsammanin za su fuskanci zafi mai tsanani sun haɗa da Kudu Maso Yamma, Taraba, Adamawa, Filato, Kaduna, Zamfara, da Sakkwato.
Zafi mai tsanani na iya zama hatsari ga lafiyar jikin mutum, yana iya haifar da matsaloli kamar bugun zuciya da zafin jiki mai yawa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta yi gargaɗin cewa bugun zuciya na faruwa ne a lokacin da jikin mutum ba zai iya daidaita zafin jikinsa ba, wanda ka iya haifar da lalacewar gaɓoɓin jiki ko ma rasa rai baki ɗaya.
Ga hanyoyi guda shida da mutum zai bi don kare kansa daga zafi mai tsanani:
1. Tufafi Marasa NauyiZaɓar tufafin da ba su da nauyi kuma masu launin haske, waɗanda aka yi da auduga su ne suka fi dacewa da wannan yanayi. Tufafin da ba su matse jiki ba suna bai wa iska damar shiga ko ina, hakan yana taimakawa wajen rage zafi.
2. Kula da ƘibaMutanen da suke da ƙiba suna da hatsarin kamuwa da cututtukan da suka shafi zafi saboda kitsen jikinsu yana hana zafi fita cikin sauƙi. Kula da nauyin jiki zai taimaka wajen daidaita zafin jiki.
3. Cin Abinci Mara NauyiZaɓar abinci masu ɗauke da ruwa kamar kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa na da matuƙar amfani a wannan yanayi. Cin abinci mai nauyi yana ƙara zafin jiki saboda yana buƙatar kuzari mai yawa wajen narkewa.
4. Gujewa Aiki A Cikin RanaYana da kyau ake zama a gida idan ana rana mai zafi sosai. Idan dole sai mutum ya fita, to yana da kyau ya fita da safe ko bayan faɗuwar rana. Sannan yana da kyau mutum ya huta idan jikinsa ya fara nuna gajiya.
5. Shan Ruwa da YawaMutum ya tabbata yana shan ruwa sosai da rana, sannan ya ci abinci masu ruwa kamar kankana, gurji, da lemu. Yin wanka da ruwan sanyi ko saka rigar da aka jiƙa da ruwa na taimakawa wajen rage zafi.
6. Rage Shan BarasaShan barasa yana sa jiki ya rasa ruwa, wanda zai iya ƙara hatsarin kamuwa da matsalolin da suka shafi zafi. WHO ta bayar da shawarar a rage shan giya ko barasa a lokacin zafi mai tsanani.
Idan aka bi waɗannan shawarwari, za a iya rage hatsarin da zafi mai tsanani ke haifarwa, tare da kare lafiya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda.
Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.
HOTUNA: An yi gobara a kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Kano Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — LauyoyiCikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar.
‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya kasance yana aiki ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce duk da tankiyar siyasa, ya ci gaba da gudanar da aiki don tabbatar da tsaro da inganta rayuwar mutanen Jihar Ribas.
Ya ƙara da cewa bayan shugaban ƙasa ya shiga tsakani domin kawo zaman lafiya, ya kiyaye duk yarjejeniyar da aka cimma, ciki har da karɓar kwamishinonin da suka yi murabus a baya.
Bayan haka, gwamnan ya ce ya amince da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke domin mayar da jihar kan turbar da doka da oda suka tanadar.
‘Majalisar dokokin Ribas ta hana ruwa gudu’Gwamnan ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatinsa ta yi domin samar da zaman lafiya, ’yan majalisar dokokin jihar sun kawo cikas.
Ya ce yana aiki ne don tabbatar da an kare dimokuraɗiyya da ci gaban mutanen jihar amma majalisar ta riƙa hana ruwa gudu.
A cewarsa, duk da saɓanin siyasa da ake fama da shi, gwamnatinsa na biyan albashin ma’aikata tare da aiwatar da manyan ayyuka don ci gaban jihar.
Fubara ya bayyana cewa duk da ƙalubalen siyasar, ya tabbatar da jihar na cikin kwanciyar hankali kuma babu wata barazanar tsaro da ake fuskanta.
A ƙarshe Fubara ya buƙaci mutanen jihar da su zauna lafiya tare da guje wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace don kare dimokuraɗiyya da tabbatar da ci gaban jihar.