Cutuka Biyar Da Ake Ɗauka A Lokacin Zafi
Published: 13th, March 2025 GMT
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi a baya-bayan nan dangane da ƙaruwar yanayin zafi a sassan ƙasar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar ƙarin matsanancin zafi.
Gargaɗin ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko huɗu masu zuwa wanda zai haddasa damuwar da yanayin na zafi kan haifar a jihohi goma sha tara na ƙasar daga yankin arewa ta tsakiya da yankin gabashin ƙasar.
Kan haka ne muka tuntuɓi likita domin ya yi mana ƙarin bayani game da cututtuka biyar da aka fi kamuwa da su a lokacin zafi da kuma hanyoyin kare kai.
Sanƙarau – Dakta Hassan Ibrahim, likita a asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya ce cutar sanƙarau na faruwa ne galibi idan aka samu cunkoson jama’a a wuri ɗaya da ya haɗu da zafi.
A cewarsa, “ƙwayoyin cuta za su shiga jikin mutum sai su shafi ƙwaƙwalwa sai a samu irin wannan.”
Zazzaɓin cizon sauro – Likitan ya ce idan yanayin zafi ya zo, mutane suna yawan buɗe jikinsu domin su sha iska. Ya ce “mutane sun fi zama a waje lokacin faɗuwar rana, lokacin da sauro ke tasiri da tafiyar da maleriya.
Hakan yana yawan taso da cutar maleriya a jikin mutane, kamar yadda likitan ya faɗa.
Fesowar ƙuraje – A lokacin zafi ne ake yawan zufa lamarin da ke janyo fesowar ƙuraje a jikn mutane wanda a cewar Dakta Hassan, idan ba a kula da su ba, “aka yi irin wata sosawa, yana iya kawo ciwo da wata ƙwayar cuta za ta iya ratsawa.”
Amai da gudawa – Dakta Hassan ya ce a irin wannan lokaci na zafi ne aka fi samun ƙuda da ruɓewar abinci. Ya ce idan ba a kula da abincin da muke ci ba, aka bari ƙuda suka yi damalmala a kai, hakan zai iya kawo ciwo a ciki idan aka ci.
Ƙonewar ruwa a jiki – A irin wannan yanayin, jikin mutum na yawan bushewa musamman a tsakanin dattijai. A cewar likitan, abin da ke sa mutum ya ji ƙishirwa, idan mutum na da rauni, ba za su samu jikinsu ya ankarar da su cewa su sha ruwa ba, ana so a riƙa shan ruwa a kai a kai.
Hanyoyin kariyaDakta Hassan Ibrahim ya ce muhimman matakan da ya kamata mutane su ɗauka wajen kare kansu daga kamuwa da cuta a lokacin zafi shi ne tabbatar da cewa ana samun yanayin “shiga da fita ta iska” ta hanyar buɗe taga a wuraren kwana da wuraren aiki da kuma rage cunkoson jama’a a wuri guda.
Ya kuma ce akwai buƙatar a riƙa amfani da gidan sauro idan za a kwanta domin kare kai daga kamuwa da cutar maleriya inda ya ce akwai buƙatar a taƙaita zama a waje da yamma.
A cewar likitan, babban matakin da ya kamata mutane su kiyaye shi ne na tabbatar da tsaftar abincin da za ake ci musamman ƴaƴan itatuwa da kuma tabbatar da tsaftar jiki.
Ƙarin wani matakin shi ne yawaita wanka a kai a kai domin rage yanayin zafi a jiki.
Sai kuma yawaita shan ruwa domin gujewa ƙonewar ruwa a jiki inda ya shawarci masu azumi da su yawaita shan ruwa da zarar sun yi buɗa baki.
Abin da ya sa aka fi kamuwa da cututtuka a yanayin zafiDakta Hassan Ibrahim ya bayyana cewa dalilin shi ne, galibin cututtuka sun fi haɓaka a lokacin zafi saboda yanayin tsaurin jiki da inda jiki ke tafiya.
“Jiki yana da yadda yake gyara kansa a duk yanayin da ya shiga, lokacin zafi yana zuwa masa da ƙarin matsi da yadda jikin zai fitar da zafi da inda zai riƙe daidai.” in ji likitan.
“A lokacin zafi, mun ƙara wa jikinmu aiki, saboda a ciki ɗumi gare shi kuma yana son ya riƙe ɗumi kuma a lokacin zafi, jikinmu yana ƙara aikin fitar da ɗumi waje yana kuma ƙoƙarin samun abin sanyi da zai iya daidaita yanayin da yake tafiyar da aikin.”
Likitan ya ce a irin wannan yanayi da jiki ke tsintar kansa a lokacin zafi, “akwai rauni da ke tasar da cutuka da za su yi tasiri.”
A cewar shi, kashi 90 na cututtuka a duniya yana da alaƙa da wani abu na sarari saboda akwai ƙwayoyin cuta da suka fi tasiri a yanayin zafi.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kariya Nijeriya yanayin zafi irin wannan
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin.
Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe.
Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a LegasWannan harin dai kai tsaye masu ruwa da tsaki na kallonsa a matsayin kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindigar da mahukuntan jihohin Zamfara da Katsina.
A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ’yan bindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar.
Yarjejeniyar sulhu da aka cimma a dajin Wurma ta samu halartan manyan ’yan bindiga irinsu Alhaji Usman Kachalla Ruga da Muhindinge da Yahaya Sani ( Hayyu ) da kuma Shu’aibu.
A ɓangaren mahukunta, akwai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi da kuma shugaban ƙaramar hukuma Babangida Abdullahi Kurfi.
’Yan bindiga sun saki wasu mutane da suke garkuwa da su a lokacin yarjejeniyar sulhun, tare da barin al’umma zuwa gonakinsu ba tare da wata fargaba ko tsangwama.
To sai dai kuma, ƙasa da wata guda bayan cimma wannan yarjejeniya, rahotanni sun ce ’yan bindiga sun kutsawa wani ƙauye a Zamfara tare da awon gaba da masallata.
Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun yi wa masallacin ƙawanya da misalin ƙarfe 5:30 na safe, daidai lokacin da jama’a ke sallar asuba.