Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya haɗa hannu da kamfanonin ƙasar Sin don samar da ingantattun fasahohin zamani da inganta noma, sufuri da ma’adanai na jihar.

 

A ranar Talata ne gwamnan ya karbi baƙuncin masu kamfanoni na ƙasar Sin a gidan gwamnati da ke Gusau.

 

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamna Lawal ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar a ziyarar aiki a ƙasar Sin daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Fabrairun 2025, domin yin haɗin gwiwa a muhimman sassa.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar ta Zamfara ta yi hulɗa da kamfanonin Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd, da Xiamen Magnetic North Technology Co., Ltd yayin da suke ƙasar Sin.

 

Tang Zhangwei, ya jagoranci wasu kamfanoni zuwa jihar Zamfara, domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a sassa masu muhimmanci, domin bunƙasa tattalin arziki.

 

A nasa jawabin, gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin da kamfanonin ƙasar Sin ke yi na tabbatar da nasarar haɗin gwiwarsu.

 

“Ina so in yi muku barka da zuwa Jihar Zamfara. Muna maraba da ku. A watan Fabrairu, na jagoranci wata tawaga zuwa ƙasar Sin don ganawa da kamfanoni a sassa daban-daban da kuma gano ci gaban da za su samar. Tafiya ce mai tasirin gaske.

 

“Mun yi haɗin gwiwa da kamfanin ƙasa da ƙasa na Zhong Zhao, wanda ya kware a fannin takin zamani da noman zamani. Suna mai da hankali kan samar da takin gargajiya da fasahar kiwo na R&D. Mun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna domin horar da manoman gida sana’o’in noma, ta hanyar amfani da injina da fasahar zamani wajen kafa masana’antar takin zamani a jihar Zamfara.

 

“Tawagar Zamfara ta yi hafin gwiwa da kamfanin Phoenix Wings, wani kamfanin ƙasar Sin da ya ƙware kan fasahar sa ido kan tsaro, gami da jirage marasa matuƙa. A tare, za su bullo da dabarun samar da ingantattun tsare-tsare na magance matsalar ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da ƙalubalen tsaro a jihar Zamfara.

 

“A taronmu da kamfanin Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd, mun tattauna batun ƙirƙire-ƙirƙire, samar da jirage marasa matuƙa da sauran fasahohi.

 

“Mun ɗauki nauyin kamfanonin Xiamen Magnetic North Technology Co., Ltd. da Xiamen King Long United Automobile Industry Co., Ltd. An gabatar da shawarwari don bunƙasa cibiyoyin sufuri na zamani da gabatar da tsarin zirga-zirgar jama’a don inganta sufuri a ciki da wajen jihar.

 

“Bugu da ƙari, mun yi taro mai nasara tare da kamfanin WEICAI LOVOL International Trading Company, wanda ke mai da hankali kan noman zamani, wanda a Turance ake kira ‘Smart Agriculture, ‘Integrated Management Platform’, da amfanin da injinan noma.

 

“Tawagar Zamfara ta gana da kamfanin Tibet Ming inda suka tattauna batun ƙara zuba jari a harkar haƙar ma’adanai, da jaddada ayyuka masu ɗorewa, ɗawainiyar jama’a, da fasahar zamani don bunƙasa haƙo ma’adinai a jihar Zamfara,” Inji Gwamna Lawal.

 

Tun da farko, sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Nakwada, wanda ke cikin tawagar jihar a ƙasar Sin, ya bayyana nasarorin da suka samu a ziyarar aiki.

 

Ya ce, “Mun kai ziyarar aiki mai inganci a ƙasar Sin, kuma sakamakon ya bayyana a yau bayan da wasu manyan kamfanoni suka zo jihar Zamfara.”

Aminu Dalhatu/Gusau

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Tsaro Zamfara a jihar Zamfara haɗin gwiwa a ƙasar Sin

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kebbi Ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantu a Jihar

Gwamnatin Jihar Kebbi ta umarci rufe dukkan makarantun sakandare na gwamnati da na kuɗi tare da dukkan manyan makarantun gaba da sakandare a faɗin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan Ilimi na Gaba da Sakandare Alhaji Issa Abubakar-Tunga da Kwamishinar Ilimi ta Firamare da Sakandare, Dakta Halima Bande, a Birnin Kebbi.

Kwamishinonin sun bayyana cewa rufe makarantun gwamnati da na kuɗi a jiha ya zama dole sakamakon hare-haren da aka kai a wasu sassan jihar kwanan nan.

Sun lissafa makarantun gaba da sakandare da abin ya shafa kamar haka:
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Dakingari da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero da Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jega da Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie da ke Argungu da Makarantar Sharar Fagen Shiga Jami’a ta Yauri.

Sai dai sun ce makarantar da kawai ba ta cikin jerin waɗanda aka rufe ita ce Kwalejin Kiwon Lafiya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Yayin da suke kira ga dukkan shugabannin makarantun da su bi umarnin gwamnati, kwamishinonin sun shawarce su da su kasance cikin natsuwa domin za a sanar da sabuwar ranar koma makarantun nan gaba.

Sani Haruna Dutsinma 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro
  • An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi saboda matsalar tsaro
  • Matsalar tsaro: Gwamnatin Yobe ta rufe duk makarantun sakandaren kwana
  • An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi na saboda matsalar tsaro
  • NAJERIYA A YAU: Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki
  • Tinubu Ya Janye ‘Yan Sanda Daga Tsaron Manyan Mutane, Ya Amince Da Daukar Sabbin 30,000
  • An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu
  • Gwamnatin Kebbi Ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantu a Jihar
  • An gano wurin da ’yan bindiga ke tsare da ɗalibai 25 da aka sace a Kebbi