Bom ya kashe mutum hudu da raunata 21 a Yobe
Published: 28th, June 2025 GMT
A ranar Juma’ar nan ne wasu abubuwa da ake kyautata zaton bom ne ya kashe mutane huɗu tare da raunata wasu 21 a hanyar Katarko zuwa Goniri a Ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe.
Kamar yadda rahoton ke nunawa, waɗanda lamarin ya rutsa da su, galibi ’yan ƙabilar Gotala ne, suna kan hanyarsu ta zuwa babbar kasuwar Buni yadi ne a lokacin da motarsu ta taka wani abin fashewa da ake zargin bam ne.
A rahoton da ya fito daga babban asibitin ƙwararru na Damaturu ya nuna cewa an kai gawarwakin mutane huɗu da suka mutu a fashewar bam ɗin zuwa gida domin yi musu jana’iza yayin da sauran ke jinya a asibitin ƙwararru da kuma asibitin koyarwa na Jami’ar Yobe da ke Damaturu.
Al’ummar Gotala dai na can ne a bakin dajin Sambisa inda ’yan ta’addan da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne suka shafe shekaru suna gudanar da ayyukansu.
Wata majiya da ba a tabbatar da ita ba ta shaida wa wakilinmu cewa, ‘yan banga da motocin soji ma sun bi ta kan wannan hanya jiya ba tare da wani abu ya faru ba.
Har zuwa lokacin cika wannan rahoto, rundunar sojin ba ta fitar da wata sanarwa ba.
‘Yan uwan waɗanda abin ya shafa da aka zanta da su a asibitoci sun yi kira ga gwamnatin Jihar Yobe da ta gaggauta sake gina hanyar da ta lalace domin daƙile ayyukan ’yan tada ƙayar baya da ke addabar al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram
এছাড়াও পড়ুন:
Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja.
Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025.
Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan lamari.
Yaƙin Gaza: Hamas da Isra’ila sun fara sakin fursunoni Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako“An gano gawar Last Kofur Femi da matarsa ne a cikin dakinsu da ke Block 15, Room 24 na Corporals and Below Quarters a Wawa Cantonment,” in ji Kyaftin Nwankwo.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a cikin sansanin kafin ya nemi izinin zuwa gida domin wasu bukatun kansa, sai daga bisani aka gano gawarsu a gida.
Kyaftin Nwankwo ya ce an ajiye gawar mamatan domin ci gaba da bincike, kuma rundunar sojan na aiki tukuru don gano musabbabin lamarin.
Rundunar Soja ta Najeriya ta bayyana matuƙar baƙin cikinta kan wannan abin takaici, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.
Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.