Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Ƙwace Iko Da Jagorancin Ƙaramar Hukuma A Katsina
Published: 26th, June 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin wani fitaccen kasurgumin dan bindiga mai suna Babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Bakatsine ne ya bayyana hakan a wani sharhi da aka wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa, maharan sun kashe mazauna yankin da dama, tare da hana ayyukan noma, da kuma haddasa durkushewar ayyukan kasuwanci na yau da kullum a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100
Wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, sun yi zanga-zangar lumana tare da neman gwamnati ta ɗauki kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Zanga-zangar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Laraba.
Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a BornoJama’a da dama sun halarci zanga-zangar; wasu a kan babura, wasu a cikin motoci, wasu kuma a ƙafa.
Kuma sun taru a ƙofar gidan gwamnatin Jihar da ke Gusau domin nuna damuwarsu.
Ƙauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka, da Fegin Mahe.
Mazauna yankunan sun ce sama da mutum 100 ’yan bindiga suka kashe a baya-bayan nan.
Wani daga cikin masu zanga-zangar, Malam Abubakar Abdullahi daga ƙauyen Fegin Mahe, ya ce ’yan bindiga sun kashe ’yan uwansa da dama, sannan kuma sun sace musu kaya da darajarsu ta haura Naira miliyan ɗaya, ciki har da buhun taki guda 500.
Hare-haren sun hana manoma yin aiki a gonakinsu, saboda rashin tsaro a yankin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gusau, Abubakar Iman, ta bakin wakilinsa Aminu Wakili Mada, ya ce ya fahimci ƙorafin jama’ar yankunan.
Ya tabbatar da cewa gwamnati tare da jami’an tsaro suna aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya, kuma za a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa wuraren da suka fi fama da matsala nan ba da jimawa ba.
Yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ci tura domin bai amsa waya ba.
A wani labarin kuma, jami’an tsaro sun ceto mutum 11 da aka sace a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.
An sace mutanen ne a ƙauyen Kaibaba da ke gundumar Turba a Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato.
An miƙa su ga Gwamnatin Jihar Sakkwato a ranar Laraba.