Sojoji sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Neja
Published: 27th, June 2025 GMT
Sojojin Sama sun kai gagarumin farmaki sansanonin ’yan bindiga da ke Jihar Neja a ranakun Laraba da Alhamis.
Wannan farmaki na zuwa ne a matsayin ramuwar gayya bayan da ’yan bindiga suka kai hari kan wasu dakarun Najeriya a kwanan nan.
’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – WikeA cikin wata sanarwa da rundunar sojin sama ta fitar a shafinta na sada zumunta, ta bayyana cewa an kai harin ne a ƙarƙashin wani shiri da ake kira FANSAN YAMMA, wanda nufinsa shi ne kawar da barazanar da ’yan ta’adda ke haddasawa.
Sanarwar, wadda ta samu sa hannun Daraktan Yaɗa Labaran rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ta ce an samu bayanan sirri cewa ’yan bindigar suna satar shanu da kuma gudanar da wasu munanan ayyuka a yankunan Kakihun da Kumbashi.
Bayan haka ne sojojin sama tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro suka gano inda suke, kuma suka kai musu farmaki.
Sanarwar ta ce, “An kai hare-haren ne nan take, inda aka kashe ’yan fashin da dama, aka lalata kayayyakin da suke amfani da su, sannan aka hana su sake haɗuwa.”
A cikin makon nan ne rahotanni suka nuna cewa ’yan bindiga sun kai hari kan sansanin sojoji a Jihar Neja, inda suka kashe aƙalla jami’an soja 17.
Rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da harin a wata sanarwa, amma ba ta faɗi adadin sojojin da suka mutu ba.
Jihar Neja na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsanancin matsalar tsaro, inda ’yan bindiga ke kai hare-hare.
Suna ƙone ƙauyuka da hallaka mutane da dama, lamarin da ke hana zaman lafiya da kuma lalata harkokin tattalin arziƙi a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya ce ko sisi gwamnati ba ta biya waɗanda suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 na sakandaren gwamnati ta Maga da ke jihar ba.
Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata, inda ya tabbatar da kubutar da ɗaliban da aka sace a farkon makon nan.
Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a KebbiYa ce, “An karɓo ɗalibanmu da aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya ba jami’an tsaro umarni su gano inda yaran suke, kuma su kubutar da su. Muna tabbatar wa iyayen yara da al’ummar Kebbi cewa ’ya’yansu sun dawo lafiya.
“Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro, musamman sojoji, ’yan sanda, da Civil Defence da suka yi aiki tukuru har aka kubutar da yaran cikin ƙoshin lafiya,” in ji Gwamnan.
Idris ya jaddada cewa gwamnatin Kebbi ba ta biya kuɗin fansa ba, “Mu, a matsayin gwamnati, ba mu ba da ko sisi ba. A binciken da muka yi, babu wanda ya biya kuɗin fansar yaran.”
A ranar Litinin din da ta gabata ce ’yqn bindiga suka sace ɗaliban su 25 daga makarantar bayan sun kashe mataimakin shugaban makarantar.
Sai dai daga bisani ɗaya daga cikin ɗaliban ta gudo ’yan kwanaki bayan sace su.