Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-06-01@01:20:49 GMT

Tambuwal Ya Raba Shinkafa Ga Gidaje Dubu 30 A Sokoto

Published: 13th, March 2025 GMT

Tambuwal Ya Raba Shinkafa Ga Gidaje Dubu 30 A Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da rabon shinkafa da sauran kayayyaki ga gidaje sama da 30,000 dake fadin kananan hukumomi 23 na jihar.

 

Da yake kaddamar da rabon a Sokoto, Sanata Tambuwal ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sake ganin watan Azumin Ramadan tare da tabbatar da ganin an gudanar da Ramadan cikin kwanciyar hankali.

 

Ya jaddada mahimmancin tunani, karamci da addu’o’in ci gaba da lafiya da wadata.

 

Tambuwal wanda shi ne Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu a jam’iyyar PDP ya ce wannan shiri na kara jaddada kudurin jam’iyyar na hadin kai, tausayi da goyon bayan al’umma a cikin wannan wata mai alfarma.

 

Ya yaba da jajircewar da jagororin jam’iyyar PDP a jihar Sakkwato suke yi, inda ya bayyana irin kokarin da suke yi na tsari, hada kai da kuma karfafa jam’iyyar.

 

Sanata Tambuwal ya jaddada kudirin sa na hadin kan jam’iyyar, inda ya bayyana aniyarsa ta dawo da aikinsu bayan zabukan da suka gabata.

 

Tsohon Gwamna Tambuwal ya kara yabawa ‘yan majalisar da aka zaba karkashin jam’iyyar PDP bisa jajircewarsu wajen yi wa mazabarsu hidima.

 

Ya yaba da yadda suke tafiyar da harkokinsu na gaskiya da kuma jagoranci na gaskiya, wanda ke nuna jajircewarsu na tabbatar da romon dimokuradiyya ga jama’arsu.

 

 

Ya kuma bukaci wadanda ke da alhakin rabon tallafin da su tabbatar da cewa tallafin ya isa ga wadanda suka amfana, kamar yadda aka tsara.

 

Tun da farko, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Bello Muhammad Goronyo, ya godewa Sanata Tambuwal bisa wannan karimcin da ya ce zai taimaka matuka wajen rage wahalhalun da ke tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a jihar.

 

Goronyo ya kara neman hadin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar domin ganin an samu gagarumin rinjaye a zaben 2027 a dukkan matakai.

 

 

 

NASIR MALALI

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Tambuwal jam iyyar PDP Tambuwal ya Tambuwal Ya

এছাড়াও পড়ুন:

MDD: Yankin Gaza Ne Ya Fi Ko’ina Fama Da Yunwa A Doron Kasa

MDD ta yi gargadi akan yunuwar da mutanen Gaza suke fama da ita, sannan ta kara da cewa:  Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji, kuma rabin cibiyoyin kiwon lafiya na yankin sun daina aiki saboda rashin isar da kayan agaji daga waje.”

 Ofishin MDD wanda yake kula da ayyukan agaji ne ya yi wannan gargadin, sannan ya kara da cewa: Yankin Gaza shi ne wurin da aka fi fama da yunwa a duniya baki daya.”

 Mai Magana da yawun ofishin na MDD ya ce: da akwai manyan motoci 600 da suke dauke da kayan agaji da su ka isa kan iyakar Gaza, amma asalinsu 900 ne da bisa wasu dalilai an hana su isa bakin iyaka.”

Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu abinda su ka iya shigar da shi cikin yankin na Gaza, shi ne gari kadai, kuma shi ba a dafe yake ba, dole ne sai an dafa shi, alhali dukkanin kaso 100% na mutane Gaza suna fuskantar hatsarin yunwa.”

Da akwai mutane miliyan 2.4 da suke fama da yunwa a zirin Gaza saboda rufe kan iyakokin shigar da kayan abinci da HKI ta yi.

Sai dar har yanzu duk da rashin amincewa da hakan da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa suke yi, har yanzu HKI ta ki bude iyakokin shigar da su.

Amurka da HKI, sun fito da wani tsari na raba kayan abinci wanda kungiyoyin gwgawarmaya su ka bayayan da cewa; tarko na ci gaba da kashe Falasdinawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hadin Gwiwar Sin Da Kasashe Masu Tasowa Ya Dade Da Zama Kan Gaba A Bangaren Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Waje
  • Cutar Kwalara Ta Yadu A Sudan Baya Ga Matsalar Tashe-Tashen Hankulan Da Suke Ci Gaba Da Yuduwa A Kasar
  • Gwamnatin Jihar Gombe Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Domin Gina Mayankar Dabbobi
  • Macron : Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba
  • MDD: Yankin Gaza Ne Ya Fi Ko’ina Fama Da Yunwa A Doron Kasa
  • Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince Da Dokokin Ilimin Noma da Gyaran Kotunan Gargajiya
  • Gasar Wasanni Ta Kasa Wata Hanya Ce Ta Hada Kan Matasan Nijeriya– Obasanjo
  • Sanarwar Bayan Taron Kolin Sin Da ASEAN Da GCC Ta Yi Nuni Ga Burin Kara Dunkulewa Waje Guda
  • Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Ayukka 16 A Sakkwato
  • ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su