Xinjiang Ta Bude Hanyar Jigilar Kayayyaki Ta Kasa Da Kasa Zuwa Afirka Ta Farko
Published: 28th, June 2025 GMT
A yau Jumma’a 27 ga watan Yunin ne a hukumace aka bude hanyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa da za ta rika aiki a kai a kai, daga Urumqi, yankin jihar Xinjiang ta kasar Sin zuwa Addis Ababa na kasar Habasha. Wannan kuma ita ce hanyar jigilar kayayyaki ta farko daga Xinjiang zuwa Afirka da kuma tasowa daga can.
Hanyar jigilar kayayyakin daga Urumqi zuwa Addis Ababa na gudanar da tafiye-tafiye na zuwa da dawowa kowace Litinin da Alhamis. Bude sabuwar hanyar ba wai kawai ya kaddamar da wata hanya ce mai sauri ta yadda ‘ya’yan itatuwa masu inganci da sauran kayayyakin aikin gona na musamman na jihar Xinjiang za su isa Afirka kai tsaye ba ne, har ma ya samar da sauki ga kayayyaki irin su ingantaccen naman sa, da naman rago, da gahawa (coffee) da sauran kayayyaki daga Habasha da sauran kasashen Afirka wajen shiga kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Za A Inganta Fannin Lafiya Da Sauran Ababen More Rayuwa A Sule Tankarkar
Majalisar zartarwa ta karamar hukumar Sule Tankarkar dake Jihar Jigawa ta amince da gudanar da muhimman ayyuka a bangarorin kiwon lafiya da sauran aikace-aikacen ci gaban al’umma.
Taron majalissar bisa jagorancin shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, ya kuma amince da gina makarantun Tsangaya guda 3 na zamani da za’a sanyawa sunayen wasu fitattun yan siyasa na yankin da suka rasu.
Yayi bayanin cewar, za’a gina makarantun tsangayar ne a garuruwan Danzomo da Shabaru da kuma Rukutu wadanda za’a sanyawa sunan wadanda suka rasu da suka hada da marigayi Sanata Dalha Ahmad Dan Zomo da marigayi Musa Waziri Kamus da kuma marigayi Ali Ado.
Haka kuma majalisar ta amince da gyaran masallatan Juma’a na Hannun Giwa da Dan Ladin Gumel da masallacin Tsangaya na Sule Tankarkar.
Alhaji Tasi’u yace za’a gina sabbin masallatan kamsisalawati guda 5 a garuruwan Chiromawa da Kofar Yamma da kuma Babban Sara.
Majalissar ta kuma amince da gina asibitoci matsakaita guda 3 a Dan Makama da Mabia da kuma Sarkin Gandu.
Shugaban karamar hukumar yace za’a gina magudanan ruwa da kuma samar da ruwan sha mai amfani da hasken rana a garin Lula.
Har il! yau Majalisar zartarwar ta kuma amince da sayo kayayyakin gyaran tuka tuka na naira miliyan 11 da kuma amincewa da naira miliyan 5 da dubu dari 5 domin sayen magunguna da feshin maganin sauro.
Kazalika, an amince da gyaran ofishin shugaban majalissar kansiloli da kuma ofisoshin masu bada shawara guda 7 don inganta ayyukan gwamnati a yankin.
Tasi’u, yace ayyukan na daga cikin kudirorin sa guda 5 da yayi koyi da ga cikin kudirorin Gwamna 12 domin kyautata rayuwar jama’ar yankin.
Usman Mohammed Zaria