’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina
Published: 12th, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile wani harin ’yan bindiga tare da ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Faskari.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani da ke yankin.
“Da misalin ƙarfe 1 na dare, muka samu rahoto cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani inda suka sace mutum 30,” in ji sanarwar.
Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka yi wa maharan kwanton ɓauna, sannan suka yi musayar wuta da su.
DSP Sadiq, ya ce babu wanda ya ji rauni daga cikin waɗanda aka kuɓutar, kuma jami’an tsaro sun samu nasarar dawo da wasu dabbobin da maharan suka sace.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Garkuwa hari musayar wuta
এছাড়াও পড়ুন:
Gobarar daji ta kashe mutum 24 a Koriya ta Kudu
Aƙalla mutum 24 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar ɓarna da ta haddasa.
Mukaddashin shugaban ƙasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun ƙarshen mako, inda ta laƙume wasu yankunan kudu maso gabashin kasar.
Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — AtikuHar ila yau, ta kuma tilasta wa kusan mutum 27,000 ƙaurar gaggawa bayan ta datse tituna da kuma na’urorin sadarwa kamar yadda mazauna yankunan da ke neman tsira da rayukansu suka sanar.
Wani jami’in Ma’aikatar Kare Mutane ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutum 18 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon wutar dajin baya ga waɗanda suka jikkata.
Sai dai daga bisani kafofin watsa labarai ciki har da BBC da CNN sun ruwaito cewa adadin waɗanda suka rasu ya kai 24 a dalilin gobarar.
A wani batun da ya shafi ƙoƙarin kashe wutar kuma wani jirgin sojin Koriya ta Kudun mai saukar ungulu ya faɗi da safiyar nan inda matuƙinsa ya rasu a ƙoƙarin dakile gobarar mai haddasa barna.
Alƙaluman da muhukunta suka fitar sun nuna cewa kimanin mutum 26 ne suka jikkata a dalilin gobarar dajin wadda ta ɗaiɗaita wani wurin bauta mai tsohon tarihi na mabiya addinin Buddha da ake kira Gounsa da ke yankin Uiseong.